✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasar Netherland za ta nemi afuwa kan cinikin bayin da ta yi a baya

Netherland ta taka rawar a harkar cinikin bayi na tsawon shekara 250.

A kokarin da take yi na wanke kanta daga abubuwan da ta aikata na mulkin mallaka a baya, gwamnatin Netherlands za ta nemi afuwa kan rawar da ta taka a harkar cinikin bayi na tsawon shekara 250.

Ya zuwa ranar 19 ga watan Disamba ake sa ran kasar ta mika neman afuwar kan yadda ta sarrafa bayi sama da 600,000 a zamanin mulkin mallaka.

Sai dai kungiyoyi daga tsofin kasashen da kasar ta yi wa mulkin mallaka kamar Suriname da ke Kudancin Amurka, sun soki lokacin da gwamnatin Holland ta ba da wannan uzuri.

Kasar ta ce ba a tuntube ta ba game da wannan ranar, kuma suna ganin an yanke shawarar cikin hatsari da gaggawa.

Kasashen sun gwammace a mika neman afuwar a ranar daya ga watan Yulin 2023, ranar da ake bikin cika shekara 150 da Netherlands ta dakatar da cinikin bayi da bauta.

Sai dai Fira Ministan Holland, Mark Rutte, ya shaida wa manema labarai a birnin Hague a makon da ya gabata cewa wani muhimmin al’amari zai auku a ranar 19 ga watan Disamba mai zuwa.