✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasar Qatar ta umarci a kama kuma a binciki Ministan Kudinta

Ministan dai ya jima yana na rike da mukamin tun sherar 2013

Kasar Qatar ta umarci a kama Ministan Kudinta, Ali Shareef al-Emadi a matsayin bangaren binciken da ake yi kan zargin karkatar da kudaden gwamnati da kuma yin amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba.

Kasar ta kuma sanar da sallamar Ministan daga kan mukaminsa.

Kamfanin Dillancin Labaran kasar ta Qatar (QNA) ya rawaito a ranar Alhamis cewa Babban Lauyan Gwamnatin kasar ne ya sanar da umarnin kamun bayan wasu takardun shaida sun same shi da hannu dumu-dumu a ciki.

“Ana zargin Ministan ne da hannu wajen yin amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba. Wannan binciken kuma somin-tabi ne, babba na nan tafe,” inji QNA.

Sarkin kasar ta Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani dai ya bayar da umarni sauke Ministan daga kan mukaminsa tun da farko, kamar yadda wata sanarwa daga Ofishin Sarkin ta tabbatar ranar Alhamis.

Kazalika, Sarkin ya kuma umarci Ministan Ciniki da Masana’antun kasar, Ali bin Ahmed al-Kuwari da ya maye gurbin korarren ministan ya ci gaba da aikinsa ba tare da bata lokaci ba.

Ali Shareef dai yana rike da mukamin tun sherar 2013, kuma shine ya jagoranci kula da lalitar gwamnatin kasar ta kusan Dalar Amurka biliyan 300.

Sai dai Ministan Harkokin Wajen kasar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa ana binciken tsohon ministan ne a kan matsayinsa na minista amma ba a lokacin da yake kula da lalitar kasar ba.

Kasar Qatar dai, wacce jagaba ce a fagen samar da makamashin gas ta fuskanci koma-bayan tattalin arziki da kusan kaso 3.7 cikin 100 a bara sakamakon annobar COVID-19 wacce ta rage bukatar makamashin a duniya.