✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashe 4 na son FIFA ta amince musu su shirya Gasar Cin Kofin Duniya a 2030

Kasashen su ne Argentina da Chile da Paraguay da kuma Uruguay

Kasashe hudu da ke yankin Kudancin Amurka sun mika bukatarsu ga Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), suna neman ta sahale musu su karbi bakuncin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Duniya da za a yi a shekara ta 2030.

Kasashen su ne Argentina da Chile da Paraguay da kuma Uruguay, kuma sun mika bukatar tasu ce a hukumance ranar Talata.

Yayin aikewa da bukatar tasu, sun nemi a dawo da gasar inda aka haifi kwallon kafa, kimanin shekara 100 bayan gudanar da gasar ta farko a Montevideo.

A wani biki da aka gudanar a hedkwatar Hukumar Kwallon Kafa ta Argentina (AFA) a Buenos Aires, babban birnin kasar, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kudancin Amurka (CONMEBOL), Alejandro Dominguez, ya kasance tare da sauran jami’ai daga kasashen hudu.

Alejandro Dominguez dai ya ce yana sa ran FIFA za ta nuna kara ta hanyar ba kasashen damar shirya gasar.

“Gasar Cin Kofin Duniya ta 2023 ba wai kawai gasa ba ce, lokaci ne da ya cancanci a yi biki domin murnar cika shekara 100 da fara ta.

“Mun gamsu da cewa ya kamata FIFA ta girmama tarihin magabatanmu a duniyar tamola, kuma hakan ya ta’allaka ne da gasar da aka fara shiryawa a yankinmu,” inji Shugaban na CONMEBOL.

Shi ma Shugaban Kasar Argentina, Alberto Fernandez, ya wallafa wani sako shafinsa na Twitter, inda a ciki ya ce za su bukaci kasar Bolivia ita ma ta bi sahunsu wajen neman shirya gasar.

Tun bayan gasar ta farko da aka shirya a Uruguay dai a 1930, Argentina ta karbi bakuncin gasar a 1978, sai Chile a 1962, yayin da ita kuma Paraguay ba ta taba karbar bakuncin gasar ba wacce ita ce kololuwa a duniyar kwallon kafa ba.

Kasashen dai yanzu za su fafata da bukatar Spain da Portugal, wadanda tuni suka nuna bukatar shirya gasar a tare, sannan ana hasashen su ma kasashen Saudiyya da Maroko su bayyana aniyar tasu na ba da jimawa ba. (NAN)