✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashen Afrika sun yi Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine

Wasu kasashen Afirka irin su Burkina Faso da Djibouti da Equatorial Guinea da Sao Tome sun ki halartar taron.

Najeriya da takwarorinta, ciki har da Nijar da Ghana da Masar da Morocco da Angola da sauransu, sun bi sahun sauran kasashen duniya wajen kada kuri’ar kyamatar mamayar da Rasha ke yi a Ukraine yayin zaman muhawara a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Rfi ta ruwaito yayin zaman, kasashe 18 daga Afirka sun shiga jerin kasashen duniya 35 da suka ki kada kuri’a a wajen taron, wadanda suka hada da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Habasha da Eritrea da Algeria da Zimbabwe da Afirka ta Kudu da sauransu.

Duk dai lamarin ya shafi kasashen Afrika, wasu kasashen yankin, irin su Burkina Faso da Djibouti da Equatorial Guinea da Sao Tome sun ki halartar taron.

Kudirin kyamatar wanda kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya da kuma Jamus suka gabatar gaban Majalisar, ya samu goyon bayan kasashe 143 yayin zaman Majalisar.

Ko da yake wasu manyan kasashe da suka hada da China da Indiya da Belarus da Koriya ta Arewa da Nicaragua da Syria sun kaurace wa zaman.

Kada kuri’ar na zuwa ne a daidai lokacin da kawayen Ukraine a karkashin jagorancin NATO suka gudanar da taro a Brussels na kasar Belgim domin sake duba yadda za su taimaka wa kasar ci gaba da yakar Rasha da kuma karbe iko da yankunanta da aka mamaye.