✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashen da Nnamdi Kanu ya je kafin a kama shi

An cafke shi a birnin Prague na Jamhuriyar Czech, aka taso keyarsa zuwa Najeriya.

Nnamdi Kanu, Shugaban haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB), ya ziyarci wasu kasashe kafin ya shiga hannun INTERPOL.

Kanu, wanda aka dawo da shi Najeriya a ranar Lahadi, ya bayyana a gaban Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Talata.

  1. Kotu ta tsare shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
  2. ’Yan bindiga sun harbe dan Majalisar Zamfara

Alkalin ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a ofishin jami’an tsaro na farin kaya (DSS) har zuwa ranar 26 ga watan Yuli, 2021.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda ya sanar da kame Kanu a wani taron manema labarai a ranar Talata, bai amma bai ba da cikakken bayanin yadda aka kamo Kanu ba.

Amma Aminiya ta gano cewar shugaban na IPOB ya ziyarci kasar Singapore, daga nan ya tafi Jamhuriyar Czech a ranar Juma’a, inda daga nan kuma ya nufi Burtaniya.

Sai dai, an kama shi a ranar Asabar a babban birnin Prague, na Jamhuriyar Czech, daga nan kuma aka taso keyarsa aka dawi da shi gida Najeriya a ranar Lahadi.

Wata majiya ta ce an cafke Kanu ne bayan wani bayani da jami’an DSS suka samu daga wata kasar Turai zuwa ga INTERPOL.