Kasashen da suka tsallaka zuwa zagayen kwata final a gasar AFCON | Aminiya

Kasashen da suka tsallaka zuwa zagayen kwata final a gasar AFCON

Mohamed Salah na murna bayan ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron rasa da aka karkare wasan da Masar ta doke Ivory Coast.
Mohamed Salah na murna bayan ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron rasa da aka karkare wasan da Masar ta doke Ivory Coast.
    Ishaq Isma’il Musa

Tawagar kasashe takwas kamar yadda yake a ka’idance sun samu kaiwa zagayen kwata final a gasar cin kofin Afirka da Kamaru ke karbar bakunci.

A jiya Talata ce dai Senegal da Morocco suka kasashe na baya-bayan nan da suka samu tsallakawa zagayen wasan na daf da na kusa da na karshe.

Senegal ta lallasa Cape Verde ne da 2-0, yayin da Morocco ta doke Malawi da ci 2-1.

Tuni dai Tunisiya da Kamaru da Burkina Faso da kuma Gambia suka shiga zagayen na gaba, inda Tunisia za ta kara da Burkina Faso, mai masaukin baki Kamaru kuwa, za ta kara ne da Gambia a zagayen na kwata final.

A yau Laraba kuma aka a buga sauran wasannin zagayen ’yan 16 na gasar ta cin kofin Afirka, inda kasar Masar da ta kara da Ivory Coast a karkare wasan canjaras mara ci, lamarin da ya sanya ta yi nasara bayan an kai ga bugun fanareti da ci 5-4.

Shi ma wasan da Mali ta kara da Equatorial Guinea, kunnen doki a ka yi mara ci, sai dai yayin da aka garzaya bugun fenareti, inda Equatorial Guinea ta yi nasara da ci 6-5.

A halin yanzu dai Masar ce za ta kara da tawagar Morocco a zagayen na kwata final yayin da kuma Senegal za ta kara da Equatorial Guinea.

Za a buga wasannin na kwata final a ranar 29 da 30 ga watan Janairun bana.