✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 90 na shinkafar da ke Najeriya ‘yar gida ce -RIFAN 

Shugaban kungiyar Manoma Shinkafa ta Najeriya, RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce Najeriya a karkashin mulki shugaba Muhammadu Buhari ta samu cigaba matuka a harkar noman…

Shugaban kungiyar Manoma Shinkafa ta Najeriya, RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce Najeriya a karkashin mulki shugaba Muhammadu Buhari ta samu cigaba matuka a harkar noman shikafa.

Ya ce kashi 80 zuwa 90 na shinkafa da ake ci a Najeriya tun daga 2015 zuwa yanzu a cikin gida ake noma ta.
Manoman shinkafa da suka yi asara na bukatar tallafi —RIFAN
Manoman shinkafa dubu 90 suka amfana da bashin noma – RIFAN
Za mu iya fara fitar da shinkafa badi – Kungiyar RIFAN
Goronyo ya bayyana hakan ne a gayawar da ya yi da Aminiya ranar Alhamis.
Ya ce, a lokacin da gwamnatin Buhari ta hau mulki, kadada guda kan samar da tsabar shinkafa mai nauyi tan 1.5 zuwa 2 metric, amma a yanzu takan samar shinkafa mai nauyin tan 5 zuwa 8 a wurin da ake noma ta a da.
Ya ce, “A shekarar 2015, lokacin da aka kaddamar da shirin tallafawa manoma da bashi (Anchor Borrowers Programme) ranar 17 ga watan Nuwamba, abin da muke nomawa a shekara bai wuce tan miliyan 2.5 zuwa 3 ba, amma a yau Najeriya tana noma tan miliyan 8 zuwa 11, ka ga an samu matukar cigaba.
“Nasarorin da muka samu daga 2015 zuwa yanzu suna da matukar yawa”, inji shi.
Ya ce “Kafin 2015, kowa ya san cewar daga kasashen waje ake shigowa da shinkafa ciki Najeriya, a duk wata 12, ana fitar da Naira biliyan 300 a matsayin kuden da za a canja a siyo shinkafa daga kasashen waje.
“Amma tun da Shugaba Buhari ya hau mulki ya hana fitar da kudaden da muke kiran su, fitar da aikin yi da hanyoyin samun arziki zuwa kasashen waje”.
Goronyo ya ce, “kashi 80 zuwa 90 na shinkafa da ake ci a Najeriya tun daga 2015 zuwa yanzu a cikin gida ake noma ta.
“Kaga kau ba karamin cigaba aka samu ba.”
Ambaliyar ruwa tazo sa a
Hakan kuma Goronyo ya danganta ambaliyar ruwan da ta mamaye fiye da kadadar shinkafa 450,000 da baiwa ga mutanen Arewa daga Allah.
Ya ce, “Daga farko bamu kiran ambaliyar ruwa “bala’i” saboda akwai albarka da zo da ita, yanzu kokari muke yi mu anfana da albarka da ke tattare da ambaliyar a wannan shekarar.
“Maimakon noman rani daya da ake yi a shekara, yanzu za a iya yin noman rani biyu a cikin shekara daya saboda ambaliyar, domin akwai wuraren da ba a yin noman shinkafa can a da, amma yanzu ambaliyar ruwan ta kai ruwa can kuma muna shirin fara noma a can.
“Za mu fara noman ranin farko a wuraren da ambaliyar ruwan ta kai cikin watan Nuwamba, mu kuma yi girbi cikin Fabrailu, bayan girbin sai mu dasa noma rani na biyu.
“Gwamnan Babban Bankin Kudi na Najeriya (CBN) ya ba RIFAN umurnin cewar dole a taimaka wa wajen manoma miliyan da za su iya noma kadada miliyan daya a shirin noman rani,” inji shi.
Ya kuma karyata labarin cewa shinkafar da aka yi fasa kaurinta ta cika l’Legas, ya babu wata iyakar Najeriya da wata kasa da ke a buds.