✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kaso 98 cikin 100 na ’yan Najeriya na karbar na goro – Muryar Talaka

Kungiyar ta ce cin hanci ne ummul-aba'isun matsalolin Najeriya.

Kungiyar nan da ke bin kadin marasa galihu ta Muryar Talaka ta ce kaso 98 cikin 100 na ’yan Najeriya na karbar cin hanci da rashawa.

Sakataren kungiyar, Kwamred Bishir Dauda ne ya bayyana hakan a Gusau, Jihar Zamfara, yayin zatawarsa da Aminiya a bikin ranar cin hancin da rashawa da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a duk ranar tara ga watan Disamba na kowacce shekara.

Mambobin kungiyar dai sun fita don zaga tituna rike da takardun da ke dauke da rubutun nesanta kansu da cin hanci da rashawa.

Kwamred Bishir Dauda, ya ce, “Ko a gidan mai za ka ga mutum ya je shan mai, amma baya son bin layi. Ko a wajen cire kudi a ATM, sai kaga mutum da zarar ya zo yana da mukami ko wata dama sai ya nuna yafi kowa sauri a bashi ya tafi.

“In ana so a shawo kan wannan matsala, sai an dauki mataki fiye da abin da EFCC ko ICPC ke yi wajen dakile matsalar sannan kuma a fara tun daga gida wajen cusawa yara tarbiya, a nuna musu muhimmancin aiki tukuru da gaskiya da rikon amana.”

A cewarsa, ya zama dole iyaye su dai na koya wa ’ya’yansu rashin gaskiya wajen aikata laifuffuka da magudin jarrabawa domin wasu iyayen har wayoyi suke sayawa “ya’yan su domin su yi amfani da ita wajen magudin jarabawa, har ila yau kuma wasu iyayen su kan sayawa “ya’yan nasu guraben karatu da manyan ayyuka.

Har ila yau yace akwai bukatar makarantu da ma’aikatun ilimi da hukumomin dake shirya jarabawa da su daina kawar da kai akan magudin jarabawa kamar yadda ake yakar yin lalata da dalibai mata a jami’oi domin su ci jarabawa ya kamata a matakin firamare da sakandire ma a yaki magudin jarabawa domin cin hanci ne.

Sannan ya ce kungiyar ta shiga sahun yaki da cin hancin da rashawa ta hanyar wayar da kan al’umma.

Daga nan sai Sakataren ya ce hakan ne ya kara jefa Najeriya cikin mummunan yanayin rashin tsaro inda ake ta kashe mutane ana sace su, duk a sakamakon cin hanci da rashawa.