✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasurgumin mai garkuwa da mutane ya shiga hannu a Edo

Ya kware wajen garkuwa da mutane kafin dubunsa ta cika a ranar Alhamis.

Jami’an tsaro a Edo sun cafke wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi jihar da satar mutane.

Wanda ake zargin ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar ne a ranar 1 ga Yuli.

  1. Ruwan sama zai iya jawo yawan hatsarin jiragen sama a bana – NEMA
  2. PIB: Majalisa ta amince da dokar man fetur

Wanda ake zargin ya kasance shugaban wata kungiya ta mutum hudu da suka kware wajen garkuwa da mutane, musamman a yankin Bini zuwa Auchi.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin na cikin jerin masu laifuka da rundunar ke nema ruwa a jallo.

An rawaito cewa ya yi garkuwa da wata mata mai suna Lucky Ojezele a yankin Idumwengie da ke kan hanyar Bini zuwa Auchi a ranar 5 ga watan Mayun bana.

Da yake tabbatar da kamun, kakakin ‘yan sandan Jihar Edo, SP Kongtons Bello, ya ce sun cafke mai laifin ne a yankin Aduwawa na birnin na Bini.

A cewarsa, rundunar ‘yan sandan tuni ta cafke daya daga cikin mutanensa sannan ta tura shi zuwa kotu don a yanke masa hukunci.