✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwanci: Darajar Najeriya ta daga duniya —Buhari

Saukaka bayar da takardun biza da izinin kasuwanci sun taka muhimmiyar rawa a kokarin Najeriya na habaka matsakaitan masana’antu.— Shugaba Buhari ya ce saukaka dokokin…

Saukaka bayar da takardun biza da izinin kasuwanci sun taka muhimmiyar rawa a kokarin Najeriya na habaka matsakaitan masana’antu.—

Shugaba Buhari ya ce saukaka dokokin kasuwanci ga ‘yan kasauwa baki ya daga darajar Najeriya ta zama daga cikin kasashen duniya 10 mafiya tagomashi wurin saukin kasuwanci a duniya.

A jawabinsa na Ranar Damokradaiyya, Buhari ya ce Najeriya za ta bunkasa bangaren hakar ma’adinai, ta kuma kulla huldar cinikayya da kasahsen Afirka da ma sauran duniya.

Ya ce sakamakon haka ya ba da umarnin farfado da masana’antar mulmula karafa ta Ajaokuta da hadin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa.

Shugaba Buhari ya ce aiki ya yi nisa a bangaren hakar zinare, da kuma zamantar da tsarin bayar da izinin hakar ma’adanai da tara kudaden shiga a bangaren domin dakile zurarewan kudaden.

Gwamanti a cewarsa, na kuma kokarin magance matsalar wutar lantarki ta hanyar gyare-gyare da fadada bangaren a dukkan yankunan Najeriya, domin magance matsalar na da muhimmanci ga raya masana’antu.

A cewarsa yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da kamfanin Siemens zai samar tare da rarraba megawati 11,000 daga nan zuwa shekarar 2023.