✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar masana’antar Nollywood ta yi faduwa mafi muni a tarihinta

Wannan ce faduwa mafi muni a tarihin masana’antar

Kasuwar hannun jarin masana’antar shirya fina-finan Kudancin Najeriya ta Nollywood, yanzu haka ta fadi da kaso 25 cikin 100, maimakon kaso 39 da take a farkon shekarar 2021.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wani rahoto da mujallar Inside Nollywood ta wallafa, ta ce faduwar kasuwar ta zo ne duk da cewa tsawon shekara biyu ke nan adadin masu zuwa gidan kallo bai ragu ba.

A cewar mujallar, adadin ya tsaya  yadda yake, wato miliyan 1.49, da karin mutane 7,000 ke nan a shekarar 2022.

Ta kuma rawaito cewa faduwar da aka samu a masana’antar, ya biyo bayan dagawar zuwa kallon fina-finan Turai na Hollywood, wanda ya sake rage adadin kason da Nollywood din ta samu a yawan masu zuwa gidajen kallo.

Wannan faduwa ta 2022, ta fi kowacce da aka taba samu a tarihin masana’antar ta Nollywood muni.

Mujallar wacce ita ce irinta ta farko a masana’antar, ta kuma gano a shekaru biyu da suka wuce, Nollywood ta samu dagowa da kaso 40, yayin da Hollywood ke da ragowar kaso 60 din.

A shekara ta 2021 kuwa, duk da annobar COVID-19, masana’antar ta samu rike kashi 39 na kudaden shiga a farkon shekarar, inda ta siyar da tikitin ’yan kallo guda 964,530, daga cikin guda 1,491,530 da aka siyar.

Sai dai a farkon shekarar 2022, daga tikiti 1,598,934 da aka siyar na masu kallo, guda dubu 520,656 ne na fina-finan masana’antar Nollywood, wanda ya kama kusan kaso 46 na faduwa ke nan idan aka kwatanta da 2021.

Daya daga masu wallafa Mujallar Anita Eboigbe ta ce wasu fina-finan kan samu yawon masu zuwa kallo, wasu kuma ba sa samu, abin dai ya danganta da karbuwar da shiri ya samu a makon da aka sake shi.

Ta ce, “A shekarar 2021, shirin fim din Omo Ghetto na jarumar barkwanci Funke Akindele ne ya samar da fiye da Naira miliyan 636 daga masu kallo ta intanet kadai.

“A 2022 kuma, shirin King of Thieves na jarumi Femi Adebayo ya samar da Naira miliyan 300 a gidajen kallo,” inji ta.

Eboigbe ta ce wannan faduwa abu ne da masu ruwa da tsaki ke ta hasashe kan dalilan aukuwarsa, amma dai alamu na nuna dogara da masu shirin za su dorawa makallata a yanar gizo ya taimaka matuka wajen janye kasuwar masu zuwa gidajen kallo.