✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katsina: Masari ya nada Muntari Lawal Sakataren Gwamnati

An nada shi bayan ajiye mukamin da Dokta Mustafa Inuwa ya yi domin tsayawa takarar gwamna

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya amince da nada Alhaji Muntari Lawal, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.

Ofishin Babban Daraktan Yada Labaran da Kafofin Sada Munta, Aminu Isa,  ne ya sanar hakan a ranar Talata.

Hawan Alhaji Muntari bisa wannan kujera ya biyo bayan ajiye mukamin da Dokta Mustafa Inuwa ya yi domin tsayawa takarar kujerar Gwamna a zaben 2023 mai zuwa kamar yadda doka ta tanada.

Kafin nada shi a wannan mukami, Alhaji Muntari shi ne Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Har ila yau, shi ne shi ne Daraktan Yakin Neman Zaben Gwamna Masari na shekarar 2015 da kuma 2019.

Sabon Sakataren gwamnatin shi ne jagoranci kwamitin zaben shugabannin jam’iyar APC tun daga matakin mazaba, karamar hukuma har zuwa ga matakin jiha, zaben da masana harkokin siyasa ganin an jima ba a ga irinsa, yadda aka yi aka gama ba a samu tashin hankali ba.

A yanzu dai a iya cewa, babban kakubalen da sabon sakataren gwamnatin zai fuskanta shi ne yadda zai hada ayyuka biyu a lokaci guda ba, wato, jagorancin wani sashe na jam’iyya da kuma ayyukan gwamnati na kai-tsaye.