✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katsina za ta farfado da masana’antar sarrafa darbejiya

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanya hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfani mai suna Contec Global Agro Ltd kan sarrafa ’ya’ayn darbejiya. Da…

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanya hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfani mai suna Contec Global Agro Ltd kan sarrafa ’ya’ayn darbejiya.

Da yake sanya hannu a madadin Gwamnatin Jihar, Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu, Muhktar Abdulkadir ya ce shirin ya dace da yunkurin gwamnatin jihar na farfado da masana’antun da suka durkushe a Jihar.

Mukhtar ya ce an kafa masana’antar ce mai suna ‘Neem-Pro’ tun a shekara ta 2007 lokacin tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’adua yana gwamnan jihar amma daga bisani ta daina aiki.

Ya ce masana’antar za ta taka muhimmiyar rawa wajen samar wa matasan jihar ayyukan yi da rage zaman kashe wando.

Da yake nasa jawabin, Babban Daraktan kamfanin, Thomas Cackunkal ya ce masana’antar na da karfin da za ta karfin da ake bukata.

Ya kara da cewa za kuma ta yi kokari wajen kara kwarin kasa a jihar wanda zai taimaka wa manoma wajen samun karin amfanin gona da kuma sashen da zai rika tatse man ’ya’yan darbejiyar da za a sarrafa domin yin wadansu abubuwan.

Katsina neem-pro ce kadai masana’antar da za ta iya tatso man ’ya’yan darbejiya wanda shi ne sinadari mafi tasiri a duniya wajen hada maganin kwari hatta a Amurka da sauran kasashen tura’’, inji Mista Thomas.

Ya kuma ce kamfanin zai rika sayen ’ya’yan darbejiyar daga hannun manoman jihar da za su rika tattarowa.

Kazalika Mista Thomas ya ce masana’antar za kuma ta kirkiri dakin gwaje-gwajen sanfuran kasa domin gano nau’in takin zamani da zai fi tasiri a wurin.