✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kauyuka 6 da suke rayuwa ba makarantar firamare a Yobe

Idan Allah Ya taimake su za mu yaki jahilci mu samu ilimi kamar kowa.

Kauyukan Janda da Aisa da Chana da Garin Mama da Garin Kwanja da kuma Kintikis, a mazabar Daya da ke Karamar Hukumar Fika a Jihar Yobe da suke da yawan jama’a kimanin 1,039 suna rayuwa ce babu makarantar firamare a cikinsu.

Shugaban Matasan Yankin Chana da Daya, Zubairu Buba ne ya bayyana wa Aminiya haka inda ya ce kaf din wadannan kauyuka nasu shida ba su da ko firamare, sai sun je garin Daya inda wadansu matasa ’yan asalin yankin da suka samu damar yin karatu suke da takardar shaidar malanta ta kasa (NCE) suka sadaukar da kansu wajen yin rumfar kara suna tara yaran kauyukan suna karantar da su boko da Islamiyya.

Zubairu Buba, ya ce matasan sun yi haka ne don ba da tasu gudunmawar wajen ceto yaransu daga rashin ilimi domin a cewarsa ba kowane uba ba ne yake iya daukar dansa zuwa garin Daya tafiyar kilomita biyu don karatun boko ba.

A cewarsa sun kai kokensu ga gwamnati don ganin an gina musu makaranta a yankin amma har yanzu babu labari.

Daya daga cikin malaman da suka zanta da Aminiya daga cikin wadanda suka sadaukar da kansu don koyar da yaran, Malam Ahmad Ya’u daga Basirka, ya ce suna koyar da yaran ne saboda ba da tasu gudunmawar don su samu ilimi zamani ganin cewa duk fadin kauyukansu babu makarantar boko.

Ahmad Ya’u, ya ce akalla yaran da suke koyarwa sun kai 50, kuma duka-duka kimanin wata takwas ke nan da fara wannan karantarwar saboda kada yaran su tashi babu ilimin boko.

Abin da ya sa muke koyarwa – Matasan

Da yake bayani game da assasa koyarwar, Dahiru Adamu Janda, cewa ya yi tunda su sun samu dama sun yi karatun har matakin NCE shi ya sa suka ware kansu su bakwai suna koyar da yaran don kada su tashi cikin duhun kai.

Dahiru Adamu, ya ce abin da suke karba a wajen iyayen yaran shi ne kudin alli kawai, nan ma don shi ne abin rubutun amma ba sa karbar kudi, kyauta suke yi domin Allah.

Sai dai ya yi amfani da damar wajen kira ga gwamnatin Jihar Yobe kan ta samar musu da makaranta cikakkiya, ta kuma ba su aikin yi don su samu hanyar dogaro da kansu.

Muna jin dadin karatu da muke yi – Daliban

Wadansu daga cikin yaran da muka zanta da su sun bayyana jin dadinsu kan koyar da su da matasan suka bullo da ita inda suka ce in Allah Ya taimake su za su yaki jahilci su samu ilimi kamar kowa.

Yaran sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Yobe ta taimaka ta samar musu da makarantar boko a kauyukan nasu don su zama cikakkun ’yan makaranta sannan sun nemi gwamnati ta fara biyan matasan da suka sadaukar da kansu wajen koyar da su kyauta ko da alawus-alawus ne kafin a dauke su aiki.

Garin Janda ya fi shekara 100 da kafuwa – Dagaci

Dagacin Janda, Bulama Malam Garba Yusuf, cewa ya yi garin Janda gari ne da ke da tsohon tarihi kuma akalla suna da yawan mutane kimanin 350 ban da rugagen Fulani da sauran kauyuka da suke kewaye da su.

Bulama Garba Yusuf, ya kuma ce shekarun garin yana da yawa domin garin akwai ganuwa irin na mutanen da tun lokacin da ake yaki, don haka akalla garin ya haura shekara 100 da kafuwa.

Ya ce suna kira ga gwamnati ta samar musu da makarantar firamare a yankin domin a cewarsa yaransu suna wuce shekarun shiga firamare kafin a sa su a makaranta saboda nisansu da garin da firamaren take wato garin  Daya.

Ya kara da cewa matasansu da suka samu dama suka yi karatu har matakin NCE ne ba su samu aikin gwamnati ba suke koyar da yaran garin saboda su ma su samu ilimin zamani.

Ba mu samu koke daga yankin ba – Kwamishinan Ilimi

Yayin da Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Ilimi na Jihar Yobe Dokta Muhammad Sani, ta waya, sai ya ce ba su samu koke daga  yankin ba kuma idan suka samu za su duba yiwuwar yadda za su fuskanci matsalar.

Dokta Muhammad Sani, ya ce yanzu haka Gwamna Mai Mala Buni, ya kafa kwamiti da zai fara rangadi don duba cikin gari da yankunan karkara a fadin Jihar Yobe da suke da irin wadannan matsaloli.

Ya ce nan ba da dade wa ba za su fara aikinsu idan sun gama su bai wa gwamnati rahoto a dauki mataki a kai.