✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kayan shaye-shaye ya kashe mutum 10, wasu 500 na asibiti a Kano

Gurbataccen abin sha ya kashe mutum 10, wasu 400 na kwance a asibiti a Kano.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce mutum 10 sun rasu, wasu 500 kuma na kwance a asibiti bayan da suka sha gurbatattun kayan shaye-shaye.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce mutum 50 daga cikin wadanda aka kwantar din suna fama ne da cututtuka masu hadari ga koda.

Ya bayyana cewa, “A baya-bayan nan, Ma’aiktar Lafiya ta sanar da barkewar wata bakuwar cuta mai alaka da gurbatattun kayan sha.

“Amfani da wadannan gurbattun kayan abincin na da matukar hadari ga kodar dan adam da wasu sassan jiki.”

Don haka ya ja hankalin mazauna da su guji shan kayan shaye-sayen musamman a watan azumin Ramadan domin kauce wa mummunan sakamakon da hakan ke iya haifarwa.

Tuni dai Hukumar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Jihar Kano ta fara bi kasuwanni tana kwace kayayyakin na kara wa kayan shaye-shaye armashi.

A lokacin za gayayen, Hukumar ta gano wasu daga cikin sinadaren da wa’adin aikinsu ya kare tun akalla shekarar da ta gabata.