✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kifi zabiya mai ido daya ya firgita masunci

An samu wani kifi jinsin zabiya matacce da wani babban kifi Shark ya hadiye a gabar teku a Lardin Maluku da ke kasar Indonesiya. Wani…

An samu wani kifi jinsin zabiya matacce da wani babban kifi Shark ya hadiye a gabar teku a Lardin Maluku da ke kasar Indonesiya.

Wani masunci a kasar Indonesiya ya firgita bayan samun kifin da aka hadiye mai ido daya jinsin zabiya.

Masuntan sun samu kifin mai ido daya ne bayan da babban kifi jinsin Shark ya hadiya, wanda tarkonsu ya kama.

Kafar labarai ta Yahoo News Australia ta wallafa cewa, an samu irin wannan zabiyan kifin ne a gabar tekun Maluku a ranar 10 ga Oktoba.

An samu kifin ne bayan farke cikin babban kifin da ya hadiye shi, amma aka same shi a mace.

Shi dai wannan karamin kifin yana da ido daya ne a tsakiyar kai tare da wasu fika-fikai a jikinsa.

Daya daga cikin masuntan mai suna Andy ya bayyana wa wata kafar labarai cewa: “Bayan bude cikin kifin da muka kama jinsin Shark, mun samu kanana kifi uku a cikinsa, amma daya ne siffarsa ta fita daban da saurani, saboda samunsa da ido daya a tsakiyar kai, sannan yana da launin zabiya.”

Masuntan sun mika kifin ga hukumomin gabar tekun don yin bincike yayin da rahotanni suka ce, ana iya samun kifi mai ido daya a cikin jinsin kifi Shark, kuma za a iya samun launin zabiya a cikin sauran jinsin kifi.

Masuntan sun ce, wannan ba shi ba ne karon farko da aka taba kama kifi mai ido daya.

Wani masunci dan kasar Amurka da farkon ganin wani kifi mai irin wannan siffar a shekarar 2011, bai yarda za a iya samun wani kifin mai kama da irin wanda ya gani ba.

Enrikue Lucero Leon ne ya ga kifin jinsin Shark zabiya a tekun Meziko. Masana kimiyya sun ce, abin da ya sa kifin da ya hadiyi wannan kifin bai rayu ba, shi ne saboda a cikin mahaifarsa akwai jinsin kifi mai ido daya da ba a saba gani ba.

Mako guda da ya gabata ne aka samu rahoton ruwa ya yi awon gaba da wani kifi zabiya a wani kogi da ke Birtaniya.

Wani masunci mai suna Shopfitter Jason Gillespie mai shekara 50 da yake kamun kifi da abokansa sun yi nasarar kama wani kifi zabiya lokacin da suke bakin aiki.

An auna tsawon kifi da ya kai kafa 3 da wani irin halitta sannan yana da wani irin launin fata.

Shopfitter Jason daga garin Hampshire, ya dauki hotuna tare da kifin kafin a sanar da irin jinsinsa da aka gano.

Ya bayyana wa kafafen labarai na garin cewa: “Ina tunanin tunda sun rasa launin fatar kifin da aka saba gani abu ne mai wahala a iya samun kifin da zai rayu , saboda yanayinsa, halitta ce za ta iya hadiyar irin jinsinta.”