✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kifewar kwale-kwale ta yi ajalin ’yan makaranta 8 a Ghana 

A ’yan shekarun baya-bayan nan ana samun yawaitar hatsarin kwale-kwale a kasar.

Wasu yara ’yan makaranta takwas sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwalensu a tafkin Volta da ke Kudu maso Gabashin Ghana.

Yaran sun hadar da maza biyar da mata uku, wadanda shekarunsu suka kama daga biyar zuwa 12.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa yaran sun taso ne daga kauyen Atikagome zuwa garin Wayokope inda makarantar tasu take.

Hukumomin kasar sun ce yaran na daga cikin yara ’yan makaranta 20 da ke cikin kwale-kwalen.

Hukumar Kiyaye Aukuwar Bala’o’i ta kasar ta ce tuni aka tsamo gawarwakin yaran.

Lamarin dai ya janyo kiraye-kiraye ga gwamnatin kasar da ta inganta harkokin ilimi musamman a yankuna karkara.

A ’yan shekarun baya-bayan nan ana samun yawaitar hatsarin kwale-kwale a kasar, lamarin da ake yawan alakantawa da daukar fasinjoji fiye da kima, da rashin ingancin kwale-kwalen da kuma samun guma-gumai a cikin ruwan.

Ko a watan Afrilun shekarar da ta gabata ma mutum bakwai ne suka mutu a wani makamancin wannan hatsari.