✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kifi ya hadiye dan ninkaya ya amayar da shi da rai

Dan ninkayar ya yi matukar firgita da abin da ya faru da shi.

Wani kwararren dan ninkaya mai suna Michael Packard ya tsallake rijiya da baya, bayan da wani hamshakin kifi jinsin ‘whale’ ya hadiye shi a bakin tekun Cape Cod, kafin ya amayar da shi.

Dan ninkayar da ke da rabon ganin badi ya yi matukar firgita da abin da ya faru da shi.

Michael Packard, mai shekara 56, ya shiga cikin tekun ne inda ya kai nisan zurfin kafa 45 a cikin ruwan da ke kusa da garin Provincetown a Arewacin Jihar Massachusetts a Amurka ranar Juma’a, 11 ga Yuni.

Amma sai daga bisani ya fahimci an hadiye shi lokacin da ya ji wani kaikayi kuma komai ya zama duhu.

A cewar Michael ya yi tsammanin kifin shark ne ya kawo masa hari, amma daga baya ya fahimci cewa ba ya jin alamar hakora kuma ba ya jin wani rauni.

“Kwatsam, sai na ji wani iri kamar an rufe jikina da wani marufi, abu na gaba da na sani na ga komai ya yi duhu sosai,” abin da Michael Packard ya ce ya tuno a yammacin ranar Juma’ar bayan fitowarsa daga Asibitin Cape Cod a garin Hyannis.

“Ina iya ji a jikina ina motsi da jin motsi, sai na ji kifin whale yana tauna tsokoki a bakinsa yayin da nake cikin cikinsa,” inji shi.

“Ina cikin kifin gaba daya; ko’ina ya zama duhu baki daya. Na yi tunani a cikin ba zan iya fita ba, babu yadda zan yi in fita daga nan. Na gama mutuwa ke nan.

Abin da kawai nake tunani shi ne ’ya’yana maza masu shekara 12 da 15 ne,” inji shi.

Mista Michael ya ce ya yi imanin cewa, ya kasance a cikin bakin kifin na kimanin dakika 30, amma ya ci gaba da numfashi saboda har a wannan lokaci yana dauke na’urar taimaka masa da numfashi.

Ya yi matukar sa’a, kifin ya girgiza kansa ya tofar da shi, daga nan makwabtansa suka cece shi lokacin da suke cikin jirgin ruwan.

“Na ga haske, bayan kifin ya tofar da ni, sai na fara jefa kaina gefe-da-gefe, kuma abu na gaba da na sani na gan ni a waje (a cikin ruwa),” inji Micheal Packard, wanda yake zaune a birnin Wellfleet a Karamar Hukumar Barnstable ta Jihar Massachusetts.

’Yar uwarsa, Cynthia Packard da farko ta bayyana wa jaridar Cape Cod Times cewa dan uwanta ya karye a kafa, amma daga baya ya ce kafafunsa sun yi rauni.

Charles “Stormy” Mayo, wani babban masanin kimiyya kuma masani kan kifin Whale a Cibiyar Nazarin Teku da ke Probincetown, ya shaida wa jaridar cewa irin wannan cin karo da mutum bakon abu ne.

Jinsin kifin Humpbacks bai da saurin kai farmaki yayin da Dokta Mayo ya yi hasashen cewa, haduwa ce ta hadari, saboda irin wannan kifin, kifaye ne abincinsa.

Jinsin kifin Humpback na iya kai nauyin tan 36 kuma ya kai tsawon kafa 50 (mita 15).