✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kin janye yajin aikin likitoci raini ne ga kotu – Ngige

“Amma wannan ba ni ya shafa ba, aikina kawai na gayyacesu tattaunawa.

Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Chris Ngige ya ce kin bin umarnin kotun da Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa (NARD) ta yi kan bukatar ta janye yajin aikinta raini ne ga kotu.

Sai dai ya ce Ma’aikatar Lafiya da Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami za su dauki matakin da ya dace, yayin da shi kuma zai sake yunkurin tattarosu don sake zama a teburin tattaunawa.

Ngige ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa na Politics Today na gidan Talabijin na Channels ranar Lahadi, lokacin da yake tsokaci kan yin biris din da kungiyar ta yi da hukuncin kotun.

A makon da ya gabata ne Kotun Ma’aikata ta Kasa da ke Abuja ta umarci likitocin da su koma bakin aiki har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kansu.

Ministan ya ce, “Cewa mu ba za mu janye yajin aiki ba… wannan raini ne ga kotu. Raini ne ga hukuncin da kotu ta yi.

“Amma ni wannan bai shafeni ba, Ministan Lafiya da kuma Babban Lauyan Gwamnati ne suke da ruwa da tsaki a ciki. Ni abin da yake nawa a ciki kawai shi ne na gayyace su na nuna musu yarjejeniyar da suka rattaba hannu a ofishina.

“Ko da yake a wancan lokacin sun ki su sa hannu a kai, amma uwar kungiyarsu ta NMA ta sa, sauran kungiyoyin kwararrun likitoci sun sa,” inji Ngige.