Kira ga Hukumar Yaki da Fataucin Yara | Aminiya

Kira ga Hukumar Yaki da Fataucin Yara

Assalamu alaikum Editan Aminiya. Ka taimaka min da fili a jaridarka mai farin jini don in yi kira ga  Hukumar Yaki da Fataucin Mutane da Musguna wa Yara cewa a ceto yaran da wadansu mata almajirai suke yawon bara da su a Legas. Idan ka je Unguwar Alabar Rago za ka ga mace da yaro daya ko yara 4 zuwa 5 wadanda in ka dube su sam ba su yi kama da matar ba, tunda shekarun matan sun wuce su haifi yaran. Kuma a gaskiya yaran nan suna bukatar kulawa, a karbo su a mayar da su ga iyayensu.

 

Daga Rabi’u Mohammad G. Baba Minjibir. Mazaunin Alaba, Legas, 09019281209.