✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kira ga Shugaban Kasa Buhari’

Abin kunya ne cewa Shugaba Buhari ba zai iya kai ziyara inda ake da matsala ba.

Na shigo wannan fili ne mai albarka domin in tofa albarkacin bakina a kan matsalar tsaro da ta addabi yankinmu na Arewa, kuma muke ganin akwai laifin Shugaban Kasarmu a cikin wannan abu da yake faruwa.

Babban laifinsa kuma shi ne rashin ganin Shugaban ya kai ziyara wani gari a dalilin kashe mutane da aka yi, wanda hakan yake nuna alamar kamar bai damu ba.

A ranar 28 ga Nuwamban bara, ’yan Boko Haram sun yanka manoma fiye da 40 a garin Zabarmari da ke Jihar Borno amma maimakon Shugaba Buhari ya je jaje da ta’aziyya sai muka hange shi a kasar Poland wajen kaburburan Yahudawan da aka kashe lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Sannan a ranar 6 ga Satumban bana, ’yan ta’adda a Jihar Sakkwato sun tare mota da mutane suka cinna wa motar wuta nan ma fiye da mutum 40 suka kone, amma maimakon mu ga Shugaban ya kai ziyarar ta’aziyya, sai muka hango shi a Jihar Legas a wajen kaddamar da littafin tarihin rayuwar Bisi Akande.

Sai kuma na ji wani mai kare muradun gwamnatin Buharin saboda ya ga ba ’ya’yansa ko ’yan uwansa a ciki yana cewa wai Shugaba Buhari ba zai kai ziyara inda akwai da matsalar tsaro ba, ya manta cewa lokacin da Buharin yake yawon kamfen babu wani lungu da sako da ya gagare shi shiga a kasar nan, sannan kasar Amurka wacce Najeriya take koyi da ita a bangaren dimokuradiyya, ta yi shugabannin da suke kai ziyara filin daga domin ganin halin da sojojin kasar suke ciki.

Kamar Shugaba George Bush da Barrack Obama duk sun kai ziyara kasar Afghanistan tun lokacin da yakin yake da zafi fiye da yanzu.

Sannan a nan Afirka akwai marigayi tsohon Shugaban Chadi Idris Derby Altino shi ma ya je fagen daga an fafata da shi kuma yana Shugaban Kasa.

Don haka wallahi abin kunya ne cewa Shugaba Buhari ba zai iya kai ziyara inda ake da matsala ba. Wato ke nan su mutanen da suke wurin duk abin da zai faru da su babu komai tunda su ba mutane ba ne?

Mu dai gaskiya ce mun fito mun fada mutanen da suke kewaye da Shugaba Buhari da dama macizai ne, amma shi ya kasa gane haka.

Babbar fitinar da Allah Ya jarabci Buhari da ita, ita ce rashin mashawarta nagari.

Allah Ya karya duk wani azzalumi da yake hana kasarmu ta zauna lafiya, amin.

Daga Lawal S. Zazzau Muchiya, Shugaban Kungiyar Matasan ’Yan Gwagwarmaya, Reshen Jihar Kaduna. 09035344055