✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiris ya rage a kone barawon talabijin a Abuja

Aminiya ta ga matashin zaune jina-jina saboda dukan da ya sha

Wani matashi mai kimanin shekaru 23 ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu fusatattun matasa suka yi yunkurin kone shi a kauyen Wumba da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja.

Mai gidan da abin ya faru, Misis Comfort Daniel ta ce bayan ta fita yin sayayya ne matashin ya haura katanga ya shiga falonta yana kokarin cire talabijin din a jikin bango.

“Da dana ya tambaye shi me yake nema sai ya ce wai ni na turo shi ya cire talabijin din zai gyara.

“Cikin ikon Allah sai na shigo gidan a daidai lokacin; ko da na gan shi da talabijin dina sai na kwalla ihun neman dauki”, inji Comfort.

Ta ce nan take wasu makwabtanta suka damke shi suka kuma kai shi Fadar Dagacin garin.

Aminiya ta ga matashin zaune jina-jina saboda dukan da ya sha a hannun wadanda suka kama shi.

Daga nan ne kuma Dagacin Wumba, Daniel Zhiba, ya gayyaci ’yan sandan farin kaya suka tafi da shi a cikin wata motar sintiri.