✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiris ya rage Obasanjo ya yi min ritaya shekaru 21 da suka wuce – Buratai

“Zan iya tunawa kimanin shekaru 21 da suka gabata da Obasanjo ya kusa yi min ritaya daga aiki.”

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai  ya ce kiris ya rage tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi masa ritaya daga aikin soja, kimanin shekaru 21 da suka shude.

Buratai, wanda ya ce a lokacin yana mukamin Manjo ne, ya bayyana zuwansa mukamin Laftanar Janar a matsayin wani lamari mai cike da tarihi.

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasar na jawabi ne yayin bikin damka ragama a hukumance ga wanda ya gaje shi, Manjo Janar Ibrahim Attahiru wanda Shugaba Buhari ya nada ranar Talata a Shalkawatar Sojojin dake Abuja.

Buratai ya ce, “Zan iya tunawa kimanin shekaru 21 da suka gabata da Obasanjo ya kusa yi min ritaya daga aiki. Ritaya ta bayan cika shekaru 40 ina bautawa kasa abu ne dake cike da tarihi, dole na godewa Allah a kan haka.”

Ya kuma yi ikirarin cewa Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ba za ta taba zama kamar yadda take a yanzu ba bayan tafiyarsa.

A cewarsa, rundunar ta sami karin tagomashi ta bangaren tattara bayanan sirri, kayan aiki na zamani da kuma inganta harkokin tsaro a fadin kasa a karkashin jagorancinsa.

A nasa bangaren, sabon Babban Hafsan Tsaron Kasa na Najeriyar, Manjo Janar Attahiru ya yi kira ga dakarun rundunar da su ba shi goyon baya, tare da yabawa Shugaba Buhari saboda ganin cancantarsa wajen zabo shi ya rike mukamin.