✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiristoci biyar sun musulunta a wurin wa’azin Dokta Zakir Naik a Abuja

Kiristoci biyar mata sun rungumi addinin Musulunci, a wurin wa’azin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na duniya da ke mahawara da Kiristoci, Dokta Zakir Naik…

Kiristoci biyar mata sun rungumi addinin Musulunci, a wurin wa’azin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na duniya da ke mahawara da Kiristoci, Dokta Zakir Naik a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja.
Wa’azin wanda dubban jama’a suka yi wa tsinke a babban filin wasa na kasa da ke Abuja, domin halartar wa’azin malamin dan kasar Indiya a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata,tururuwar da jama’a suka yi zuwa filin, ya tilasta jami’an tsaro amfani da dabaru daban-daban domin ganin ba a samu turmutsutsin da zai kawo matsala ba.
daya daga cikin mata Kiristocin da suka musulunta mai suna Yemisi, ta bayyana wa Shehun malamin cewa a rana ta biyu ta wa’azin cewa: “Bayan na saurari hujjoji da ka ba ni a jiya, na fuskanci magabatana da su, sai dai sun kasa gamsar da ni, saboda haka yau na dawo ina bukatar a ba ni Musulunci.”
Ana ganin sanarwar da aka rika yi a masallatai da kuma daukar nauyin kudin shiga filin wasa da aka shirya kan Naira dubu daidai da wani bawan Allah daga Kano ya yi, sun taimaka wajen dandanzon jama’a domin sauraren wa’azin na Dokta Zakir Naik da ke wa’azin Musulunci tare da kawo misali da Baibul.
Wakilinmu ya lura duk da amfani da salon ajiye motoci a kan tsari daga nesa da jami’an tsaro suka dauka, a karshe jerin gwanon motocin ya dangana da harabar filin wasan, inda aka fuskanci dakon wucewar motoci a kan hanyar filin, wadda ta sada birnin da filin jirgin Abuja da babbar hanyar da ta nufi Kudancin Najeriya.
Kiristoci da dama da suka je wurin wa’azin sun fuskanci malamin da mukabala, kuma an ba su damar yin jawabi fiye da takwarorinsu Musulmi, kuma hakan ne ya taimaka matan da suka halarci wa’azin suka mika wuya ga Musulunci, yayin da takwarorinsu maza suka jajirce tare da ci gaba da jayayya da malamin.