✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiristoci masu ziyarar ibada daga Najeriya sun isa Jordan

Sun isa kasar ce daga Isra'ila

Rukunin farko na Kiristoci masu ziyarar ibada daga Najeriya sun isa kasar Jordan a ranar Litinin, bayan shafe kwana hudu suna ziyarar wurare masu tsarki a kasar Isra’ila.

Hukumar Kula da Maniyya Kiristoci ta Najeriya (NCPC) ce ta tabbatar da hakan, yayin hirar kakakinta, Kande Ibrahim, da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Talata.

Kwamishina a hukamar NCPC, Rabaran Jidda Gelengu, ya ce kawo yanzu, ziyarar maniyyatan na ci gaba da gudana ba tare da wata wahala ko kuma cinkoso ba.

Daga nan, ya yaba wa Babban Sakataren Hukumar, Rabaran Yakubu Pam, bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da nasarar masu ziyarar a duk wuraren da suka ziyarta.

Bayan kammala ziyarar muhimman wurare a Jordan, daga nan ake sa ran maniyyatan za su dawo gida Najeriya, inji Forgiven Amachree, wanda Kwamishina ne a hukumar.

A bara ce dai NCPC ta zabi Jordan a matsayin kasar da Kiristoci masu ziyarar ibadar na Najeriya za su rika zuwa.

(NAN)