✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kirsimeti: An cire shingaye a Hanyar Kano-Abuja

Gwamnatin Tarayya ta bude sassan da aka rufe a hanyar da ta tashi daga Kano ta bi ta Kaduna zuwa Abuja baki daya domin zirga-zirgar…

Gwamnatin Tarayya ta bude sassan da aka rufe a hanyar da ta tashi daga Kano ta bi ta Kaduna zuwa Abuja baki daya domin zirga-zirgar ababen hawa a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Yanzu haka dai duk hanyar mai nisan kilomita 380 da za ta kasance a bude, daga yanzu zuwa Janairun 2023.

Daraktan Kula da Manyan Tituna da Gyare-gyare na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya, Folorunso Esan, ne ya bayyana haka a Zariya a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin hanyoyin.

“Daga Abuja zuwa Zariya, mun lura cewa babu shingaye, don haka babu shamaki ga wanda ya biyo titin daga Abuja har zuwa Kano yanzu.

“Wannan ita ce babbar hanya a dukkanin yankin Arewa maso Yamma, ko ma Arewa baki daya, don haka ba ma son samun wata matsala a wannan lokacin na bukukuwan.

“Sauran abin da da ya rage na aikin kuma, dan kwangilar zai karasa a watan Janairu.

“Don haka, yanzu, mun bude hanya don mutane su yi amfani da su.”