✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kirsimeti: Mun yi shirin ko-ta-kwana a Gombe — ’Yan sanda

Rundunar ta kuma ce za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro a jihar

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, ta ce ta yi tanadi na musamman da hadin guiwar sauran jami’an tsaro don dakile duk wani rikici da zai iya faruwa a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Oqua Etim, ne ya ba da tabbacin a Gombe, inda ya ce hakan na cikin irin kokarin rundunar na ganin an yi bukukuwan lami lafiya.

Ya kuma ce an haramta sayarwa da kuma amfani da duk wani nau’in abin fashewa nai kara da ya shafi na wasan wuta wato ‘Knockout’, da dai sauransu.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Jami’in hulda da Jama’a na rundunar a Jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan.

Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana sayar da nau’in kayayyakin da aka haramta din zai fuskanci fushin hukuma.

Kwamishinan ya kuma umarci Kwamandojin Shiya da Turawan ’Yan Sanda (DPO- DPO) da duk wasu shugabanin sashi na rundunar da su baza jami’an tsaro na sirri a duk inda ya dace don samun sirri a kuma ajiye wasu a manyan hanyoyi, sannan a samar da motocin silke na sintiri don samar da tsaron da zai ba da dama na gudanar da bukukuwan cikin lumana.

Sannan sai Kwamishinan ya yi kira ga shugabanin al’umma da iyaye da su kula da ’ya’yansu sannan su dinga kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga hukuma mafi kusa.

Oqua Etim ya kuma hori masu ababen hawa da su kiyaye dokokin hanya sannan su guji gudun wuce sa’a da kuma daukar kaya fiye da kima.