✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kirsimeti: Mutum 2 sun nutse a teku, an samu gobara 24 a Legas

Wasu mutum biyu sun nutse a gabar teku, a yayin da aka samu rahotannin tashin goba 24 a Jihar Legas a lokacin bikin Kirsimeti. Rahotanni…

Wasu mutum biyu sun nutse a gabar teku, a yayin da aka samu rahotannin tashin goba 24 a Jihar Legas a lokacin bikin Kirsimeti.

Rahotanni na nuna cewa wasu matasan sun rasa ransu a lokacin da suke kokarin ceto mutum da ya fada a gabar tekun Baracuda a kusa da unguwar Abraham Adesanya da ke yankin Ajah na jihar.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), ta ce jami’inta da ke wurin ya sanar da ita cewa, wurin da mutanen suka je ceto mutumin waje ne mai hadari sosai.

Har zuwa lokacin tattara labarin nan dai ba a kai ga gano gawarwakin mutanen ba.

A halin da ake ciki dai an samu karuwar kiraye-kirayen gaggawa a lokacin bikin Kirsimeti.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana cewa ta kai agaji akalla wurare 24 a ranar Kirsimeti kadai.