✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Fulani: Babu ruwanmu a sintirin Amotekun —Miyetti Allah

Sai da jami'an Amotekun suka yi wa Fulani aika-aika kafin aka sanar da mu

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta karyata masu cewa ta yi sintirin hadin gwiwa da jami’an tsaro na Amotekun a Jihar Oyo, inda suka kai samame tare da kashe wasu Fulani da ake zargi da garkuwa da mutane.

Wasu daga cikin shugabanin Miyetti Allah a Jihar ta Oyo sun ce babu ruwan kungiyar, suka kuma bayyana mamakin samamen da aka kashe Fulani a kauyen da mutane ke zaune sama da shekara 45 da sanin hukumomi.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar da ya bukaci a boye sunansa ya ce sun dai tattauna da shugabannin Amotekun inda bangarorin suka “amince a kan wuri da kuma lokacin da za mu hadu amma muka yi ta jiran su ba su zo ba.”

Jami’an Amotekun sun kashe Fulani uku da suka hada da Alhaji Usman Okebi da ’ya’yansa biyu a kauyen Okebi da ke Karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa a Jihar.

Wasu rahotanni sun ce an yi dauki ba dadi ne tsakanin ’yan Amotekun da mazauna kauyen na Okebi.

Sai dai Kwamandan Rundunar Amotekun na Jihar Oyo, Kanar Olayinka Olayanju (murabus) ya ce babu wani rikici da aka yi tsakanin jami’ansa da Fulani makiyaya a yankin Ibarapa da Oke Ogun na Jihar.

Samame shida

Kwamandan ya shaida wa manema labarai cewa rundunarsa dai ta kaddamar da ayyukan sintiri guda shida a kananan hukumomi hudu na jihar.

Ya ce ’yan bindiga sun kai wa tawagar da aka tura Aiyete, amma jami’an suka yi nasarar kashe uku daga cikin maharan bayan sun gwabza fada.

A cewarsa, dukkannin ayyukan sun samu goyon bayan al’ummar Fulanin yankunan kuma wasu daga cikin ’yan kungiyar Miyetti Allah sun shiga an yi aikin da su.

“Sabanin duk wani rahoto da kuke samu, babu wani rikici da aka yi tsakanin Fulani makiyaya da Amotekun a yankin Ibarapa ko Oke a Jihar Oyo.

“Abin da ya faru shi ne mun kaddamar da ayyukan tsaro a dazukan kananan hukumomin da ke famda da matsalar garkuwa da mutane da kashe-kashe a baya-bayan nan.

“Da mutanenmu sun shiga Aiyede san aka kai musu hari, inda aka yi musayar wuta har aka kashe uku daga cikin maharan, wani jami’inmu kuma ya samu rauni.

“Ba da Fulani aka yi fada ba saboda Fulani na cikin wadanda suka shirya aikin, da su muka yi aikin sharar dazukan, kuma Amotekun na aiki ne kafada-da-kafada da kungiyar Miyetti Allah,” a cewarsa.

‘Mutanen ba su ji ba, ba su gani ba’

Amma daya daga cikin jagororin Miyetti Allah da muka zanta da shi ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa babu yawunsu a abin da ya faru.

“Tabbas mun yi zama tare da shugabannin Amotekun inda muka amince mu yi aikin samar da tsaro tare.

“Sun shaida mana cewa an yi garkuwa da wasu mutane kuma suna so su je su yi aikin ceto su.

“Muka ce musu hakan ya yi daidai, amma zai fi kyau a sanya cikin aikin sosai saboda mazauna wasu yankunan da za su shiga ba sa jin Yarbanci, jami’an Amotekun kuma ba sa jin Fillanci ko Hausa.

“Muka kuma bayyana musu cewa dole su yi taka-tsan-tsan kar su yi kuskuren daukar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a matsayin masu garkuwa da mutane,” inji shi.

Shi ma wani jami’in kungiyar ta Miyetti Allah ya ce, an kira su ne ana neman ceto ne bayan da aka riga an yi wa al’ummar Fulanin barna.

“An kira ne ana shaida mana cewa jami’an Amotekun sun kashe mutanenmu, mu kuma muka sanar da hukumomin da suka dace,” inji shi.