✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Hanifa: An fara sauraron shaidu a Kotu

Lauyan wadanda ake kara ya yi suka game da shaidun bayan ya yi musu tambayoyi.

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako karkashin jagorancin Mai shari’a Usman Na’abba ta fara sauraron shaidun masu gabatar da kara game da shari’ar da ake yi a kan kisan Hanifa Abubakar.

Aminiya ta ruwaito cewa ana dai tuhumar Abdulmalik Tanko da Hashim Isyaku da Fatima Jibril Musa da laifin hadin baki da yin garkuwa da mutane da boyewa da kuma kisan dalibarsa Hanifa Abubakar ’yar kimanin shekaru biyar da haihuwa.

Masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Musa Abdullahi Lawan sun gabatar wa kotu shaidunsu na farko da na biyu wato jami’an Hukumar DSS wadanda su suka kama wanda ake zargi na farko a daidai lokacin da yake yunkurin daukar kudin fansar da aka ajiye a rukunin Gidaje na Khalifa Isyaku Rabiu da ke kan titin Zariya.

Haka kuma, masu kara sun gabatar wa kotu shaidarsu na uku – dan sanda da ya jagorancin bincike a kan lamarin, wato insfekta Ubale Usman wanda ya shaida wa kotu cewa su suka karbi lamarin tun daga lokacin da iyayenta suka sanar wa Rundunar ’Yan sanda labarin bacewar ’yarsu har zuwa lokacin da aka kama wanda ake zargi na farko har zuwa lokacin da aka hako gawar Hanifa da kuma lokacin da aka kai gawar Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed.

Insfekta Ubale Usman ya ci gaba da bayyana wa kotu cewa lokacin da ya yi wa wanda ake zargi tambayoyi ya bayyana masa cewa shi da kansa (Abdulmalik) ya dauki Hanifa a daidai lokacin da ta taso daga Makarantar Islamiyya bayan wadanda ake zargi na biyu da ta uku suka kasa dauko ta a karo na farko.

Insfekta Ubale Usman ya shaida wa kotu cewa Rundunar ’Yan sanda sun karbi rigar Makarantar Islamiyya ta Hanifa da Hijabinta da bajo da kudi Naira dubu talatin da dari uku wanda aka karba a hannun wanda ake zargi na farko da na biyu da kuma shebur da aka yi amfani wajen hako gawar Hanifa.

Kazalika, ’yan sanda sun gabatar wa kotu wayoyin da suka karba daga hannun wanda ake zargi na farko da ta mahaifiyar Hanifa da wasu wayoyin guda biyu da wanda ake zargi na farko ya karba a hannun wasu almajirai ya yi amfani da su wajen kiran mahaifiyar Hanifa a lokacin yana neman kudin fansa.

Haka kuma ’yan sanda sun gabatar wa kotu hotunan kabarin da aka binne Hanifa da kuma na lokacin da ake hako gawarta.

Lokacin da aka nuna wa wadanda ake zargi dukkanin wadannan kayayyaki sun tabbatar da cewa sun san su.

Sai dai lauyan wadanda ake kara Barista Labaran Usman ya yi suka game da shaidun bayan ya yi musu tambayoyi, wanda  a kan haka ne Mai shari’a Usman Na’abba ya dage zaman shari’ar zuwa ranar Alhamis don ci gaba da sauraron shaidun.