✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Hanifa: Dalilin da aminci zai kau tsakanin iyayen dalibai da malamai

Wannan ba zai hana iyaye su kara lura sosai ba, kada su gaskata duk wani mahaluki.

A yayin da har kawo yanzu kura ba ta lafa ba dangane da kashe yarinyar nan mai shekaru biyar da aka yi a Jihar Kano, al’umma na ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta da kuma tsokaci a kan lamarin.

Haka kuma an samu da dama da ke yin tofin Allah-tsine a kan kisan da aka yi wa yarinyar.

A makon jiya ne dai aka gurfanar da Abdulmalik Muhammad Tanko, malamin makarantar da ake tukuma da garkuwa da kuma kashe dalibarsa ’yar shekara 5 Hanifa Abubakar.

Aminiya ta ruwaito cewa, Abdulmalik ya bayyana gaban kotun ne tare da mutane biyu, Hashimu Ishiyaku, da Fatima Jibrin Musa da ake zargi suna da hannu a garkuwa da kuma mutuwar Hanifa.

Mutumin da ake tuhuma dai ya ce da shinkafar bera ta N100 ya yi amfani wajen kasheta.

Wanda ake zargin dai shi ne mai makarantar Noble Kids da ke Kano, kuma ya kashe yarinyar ne bayan ya sace ta, sannan ya yi yunkurin karbar kudin fansa daga iyayenta.

Tun farkon watan Disamban bara ne aka sace Hanifa lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makarantar Islamiyya.

Malamin dai ya bukaci a biya shi Naira miliyan shida a matsayin kudin fansarta, inda a wajen karbar kudin ne dubunsa ta cika.

Sai dai ko a lokacin da yake kokarin karbar kudin fansar ma ya riga ya hallaka ta, amma ya ki shaida wa iyayenta.

To sai dai bayan kama shi, wanda ake zargin ya shaida wa ’yan jarida a hedkwatar ’yan sandan Kano cewa da shinkafar bera ta N100 ya yi amfani wajen kashe yarinyar.

A zantawar da Aminiya ta yi da Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata, babban darektan cibiyar wayar da kan al’umma a kan muhimmancin shugabanci na gari da kuma tabbatar da adalci (KAJA), shi ma ya yi tsokaci kan tasirin wannan lamari a tsakanin masu da ruwa da tsaki.

Ya ce idan aka dubi wannan al’amari da ya faru, sai ka ga ya kara nuna cewa iyaye babu wani mahaluki da ya rage da za su yarda da shi ko kuma za su nuna wa ’ya’yansu su yarda da shi, domin idan aka yi la’akari, tun farko an tsinci kai ne a wani yanayi na cewa irin wannan satar mutane da ake yi musamman kananan yara, an fi amfani da sanayya.

Ko dai a sace su a kashe su, ko a sace su a yi musu barna ta hanyar lalata musu rayuwa kamar saduwa da su da sauransu.

Wannan wani abu ne da ya dade, saboda mun sani cewa, ko a ’yan kwanakin baya akwai yarinyar da a yankin unguwar Birged a Jihar Kano, irin wannan ta taba faruwa cewa wacce aka yarda da ita tana shiga gidansu har tana yi wa mahaifiyarta kitso, ita ce ta bi ta Islamiyya ta dauke, ta hada baki da wasu, har aka yi sanadin rayuwar yarinyar.

Yanzu kwana-kwanan ga shi, shi ma wani a Zariya wani yaro wanda ana zargin makwabcin mahaifinshi ne, bayan ya karbi kudi, kimanin fiye da naira miliyan hudu, shi ma ana tunanin yaron makwabinsu ne ya sace shi kuma ya halaka shi.

Mu kanmu a nan cikin Karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano, kwanaki duk an samu sace-sacen yara wanda za ka duba duk wanda asirinsu ya tonu, za ka ga mutane da suke jikin iyalan irin wadannan yara, saboda haka wannan shi ya nuna cewa babu wani mahaluki da don yana da dangartaka da mutum ko yana da wata alaka, a saki jiki a nuna wa yara cewa wannan mutumin a gaskata shi.

Domin yanzu ba ga makwabci ba, ba ga dan uwa na mahaifi ba, ba ga dan uwa na mahaifiya ba, ba ga malamai ba, babu wani mutum da za a gazkata.

Amma abin da nake so mutane su fahimta, gaskiya ne shi wannan Abdumalik Muhammad Tanko wanda ya kashe Hanifa, ya yi amfani da cewa ya san Hanifa, ya bita makarantar Islamiyya, amma ai shi malaminta ne na makarantar boko ko kuma shi ne ma mai makarantar.

Amma me ya sa a lokacin da Hanifa ta zo makarantarshi ta boko bai yi abin da yake so na sace ta ba, ka ga a nan amana ce tsakanin malami da iyayen yarinya, lokacin da aka turo ta makarantar boko, sai ya ki ya yi amfani da wannan amanar da aka ba shi saboda shi ne zai kwana a ciki duk binciken da za a yi da shi za a yi domin a makarantarsa ta bata.

Sai ya bari sai da ta tafi makarantar Islamiyya, tukunna ya bi ta, wadda a yadda iyayen Hanifa suka fada, kwana daya da batan Hanifa yana daga cikin mutanen da suka je suka jajanta musu har yana zubar da hawaye, wanda saboda wannan bincike ba zai kai kan shi ba.

To saboda haka, wannan zai sa iyaye su yi shakku sannan kuma su ji tsoron kulla alakar ’ya’yansu da malaman makarantansu.

Amma idan muka duba sosai, alakar ba ta na yiwuwa ba ne lokacin da ka mika ’ya’yan nan naka a makarantar da wadannan malaman suke, wannan abun ya faru ne ba a makarantar da shi Abdulmalik Muhammad Tanko ya ke koyarwa ko mallakinsa, a’a wani wuri ya bi ta.

Ya yi amfani da sanayyar da ke tsakaninsa da ita, maimakon ya je ya yi ta dibi-dibi yana so ya saci wani yaron ko wata yarinyar, sai ya bi ta saboda shi yana da wasu bayanai a kanta, ya santa, ya san iyayenta, ya san inda take islamiyya, wanda wannan ne ma ya sa lokacin da ya je zai dauke ta, har take magana tana kiran shi da Uncle, wanda kuma ga bisa bayanan wadanda suka so su taimaka mi shi ya sace ta, su da suka je saboda ba ta sansu ba, sai ya kasance su ba su iya sun sace ta ba.

Saboda haka gaskiya ne, iyaye ba za su gaskata kowane mutum ba saboda yadda tsari na rayuwa ya lalace, amma wannan abun da ya faru na Hanifa, malaminta na makaranta, ba ya faru ba ne a makarantar, wanda amanar da ke tsakanin iyaye da dalibai tana kulluwa ne a makarantar nan abin da ya hada su shi ne wannan makarantar, yayin da suka zo makaranta, to amana ta kullu, amma idan ba sa makarantar, ba sa hannun malaman nan nasu na makarantar boko, sai dai ko tana hannun malamansu na Islamiyya.

Saboda haka shi ya yi amfani da amincewa da ita yarinyar ta san shi, da kuma sanin wasu bayanai da ya yi game da ita, ya bita kamar yadda aka samu wasu mutane makwabta da ’yan uwa suna fakar idon iyaye suna bin yara inda aka aike su ko kuma inda aka tura su makaranta suna sace su ko su lalata musu rayuwa ta hanyar aikata alfasha da su ko kuma su nemi kudin fansa su sake, a wasu lokutan ko kuma su kashe su.

Saboda haka abin da yake faruwa, zamani ya zo da cewa babu wani mahaluki da za a gaskata, kowa ya yi kaffa-kaffa yana nuna wa ’ya’yansa cewa kada su sake su amince da wani mutum ko waye idan ya gansu an aike su, makaranta ko an aike su siyan wani abun ko wani wuri, ya ce musu zo mu je wani wuri su yarda da shi.

Ta wani bangaren kuma, ni bana tunanin wannan zai kara taba alaka sosai da take tsakanin malamai da kuma yara, domin ai ba ya faru ba ne a makarantar da yake koyarwa, ya dai yi amfani ne da wata kafa ta cewar an san shi, ya bi Hanifa makaranta, duk da cewa wannan ba zai hana iyaye su kara lura sosai ba, kada su gaskata duk wani mahaluki, domin ana amfani ne da sanayya, da malunta, da makwabtaka, da ’yan uwantaka, ana muzanta wa yara ana sace su har tana kai ga halaka su.