✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Hanifa: An mayar da shari’ar gaban Babbar Kotu

Za a ci gaba da shari'ar mutanen da ake zargi a gaban babbar kotu ranar 9 ga Fabrairu, 2022

Kotun Majistare mai lamba 12 da ke Kano ta bayar da umarnin mayar da shari’ar kisan gillar da aka yi wa Hanifa Abubakar mai shekara biyar zuwa gaban Babbar Kotun Jiha.

Tun da farko mai gabatar da kara, Barista Aisha Mahmud, ita ce ta yi wannan roko a gaban kotun inda ta shaida wa kotun cewa duba da cewa kotun ba ta da hurumin yin shari’ar kisa, don haka sun kammala rubuta caji game da tuhumar da ake yi wa wadanda ake zargin, sun kuma mika cajin gaban babbar kotu don fara sauraren shari’ar.

“Mun nemi kotu ta dage wannan shari’a ne domin wannan kotun ba ta da hurumin yin shari’ar laifukan da ake zargin wadannan mutane da aikatawa, saboa haka za mu gurfanar da su gaban Babbar Kotun Jiha karkashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na’abba,” inji shi.

Ana dai zargin Abdulmalik Tanko da Hashim Isyaku da Fatima Jibrin da laifukan hadin baki da yin garkuwa da mutane da boyewa da kuma kisa, wadanda laifuka ne da karkashin sashe na 97 da 274 da 277 da 221 na Pinal Kod.

Alkalin Kotun Mai Shari’a Muhammad Jibrin ya bayar da izinin sake gurfanar da wadanda ake zargin gaban babbar kotun jiha.

Ya kuma ba da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu, 2022.