✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Hanifa: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci

Kotun ta tsaida ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a titin Audu Bako ta tsaida ranar 28 ga watan Yuli a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar Hanifa Abubakar da ake zargin malaminta, Abdulmalik Tanko da yi mata kisan-gilla.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Usman Na’abba ne ya tsaida ranar a zaman kotun na ranar Talata, bayan gabatar da shaida da kuma sauraren kowane bangare.

Tun farko an gurfanar da Abdulmalik tare da Hashim Isyaku da Fatima Jibril Musa a gaban babbar kotun, inda ake tuhumarsu da aikata laifuka guda biyar da suka hada da hada baki, aikata garkuwa, tsarewa da kuma kisan-gilla, wanda hakan ya saba da sassa na 97 da 274 da 277 da kuma 221 na kundin laifuka na penal code.

A zaman da kotun ta yi a ranar Talata, mai shigar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba Soron Dinki, ya bukaci kotun da ta yi la’akari da shaidun da aka gabatar a gabanta kan wadanda ake tuhuma tare da bukatar yanke musu hukuncin kisa.

“Muna kira ga kotu da ta zartar da hukuncin kisa a kan wadanda ake tuhuma saboda laifin da ake tuhumarsu da shi hukuncin kisa ne ya dace da shi,” inji shi.

Aminiya ta ruwaito yadda aka sace Hanifa a ranar hudu ga watan Disamban 2021 a kan hanyarta ta komawa gida daga makarantar Islamiyya, wanda daga baya aka gano cewar an kashe ta.

Da farko Abdulmalik Tanko ya amsa laifin yin garkuwa tare da kashe ta, ta hanyar ba ta gubar Naira 100 sannan kuma ya birne ta a wani rami a daya daga cikin makarantunsa.

Amma daga bisani ya musanta laifin kashe ta a gaban kotu, inda ya bayyana cewar bai san yadda aka yi ta mutu ba.