✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Hanifa: Kotu za ta yanke wa Abdulmalik hukunci

A yau ne ake sa ran kotu za ta yanke hukuncin karshe kan shari’ar kisan yarinyar nan da ake zargin shugaban makarantarsu ya yi wa…

A yau ne ake sa ran kotu za ta yanke hukuncin karshe kan shari’ar kisan yarinyar nan da ake zargin shugaban makarantarsu ya yi wa kisan gilla, Hanifa Abubakar.

A watan Janairun 2022 ne dai aka gurfanar da Malam Abdulmalik Tanko da mutanen da ake zargin su tare a gaban kotu, kan zargin hada baki wajen sace karamar yarinyar da kuma kashe ta.

Ana tuhumarsa ne da sace Hanifa ne daga wani reshen makarantar Abdulmalki unguwar Kawaji da ke ’Yankaba a birnin Kano a watan Disamba.

Ana zargin sun sace yarinyar ce hanyarta ta komawa gida daga islamiyya, inda Abdulmaliki ya kai ta wata makarantarsa mai suna North West, da ke Tudun Murtala, inda ya kashe ta, ya kuma binne gawarta a harabar makarantar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a A Daidaita Sahu suka tafi da ita, kuma an yi ta nema da cigiya amma sai bayan kwana 46 aka samu jin duriyarta.

Sai dai daga baya an saki sauran wadanda ake zargin, amma aka cigaba da tsare Abdulalik Tanko, bayan wanke sauran da kotun ta yi.

Kisan Hanifa dai ta jawo tofin Allah tsine daga mutane daga kowane bangare, ciki har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da matarsa Aisha da manyan shugabanni da suka bukaci a kwatar wa Hanifa hakkinta a gaban shari’a.

Haka kuma an samu wasu da suka fusata da lamarin suka babbake makarantar Abdulmalik din, wanda ya zuwa yanzu babu wanda aka kama kan lamarin.

Labarin Hanifa ya karade ciki da ma wajen Najeriya, kuma mutane sun zuba ido don ganin irin hukuncin da hukumomi za su yanke wa mutumin kan aika-aikar.