✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Harira: IPOB na kokarin rura wutar rikicin addini – CAN

CAN ta ce dole a dakike hare-haren IPOB don kada ta haddasa yakin basasa

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), ta yi Allah wadai da kisan da ’yan awaren Biyafara (IPOB) suka yi wa wata mata da yaranta hudu, inda ta ce kungiyar na kokarin haddasa yakin basasa da na kabilanci.

Adebayo Oladeji, mai magana da yawun shugaban (CAN), Samson Ayokunle ne, y sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce IPOB na fafutukar kafa kasa ga matattu ne ko me?

“Su sani cewa laifin da suke aikatawa ba sa taimakon shari’ar shugabansu, Nnamdi Kanu. Bai kamata su mayar da Kudu maso Gabas tamkar yankin da ba wanda zai zauna ba, domin maslahar iyayen da suka kafa kasar nan.

“Ayyukansu ba wai iya kawai bata sunan Ndigbo su ke yi ba, suna shirin haifar da yakin basasa da fadan addini. Shin wacce kungiya mai hankali za ta rika aikata laifuka irin wadannan?”

CAN ta kuma bayyana cewa: “Tabbas wannan laifi ba abun a yaba bane, da CAN da duk mai hankali ba zai goyi bayan wannan ba. Muna kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kansu.

“Yanzu masu aikata wannan laifuka suna tunanin sun yi daidai, yayin da wadanda ake sa ran za su dakatar da su ko kama su sun nuna ba su da ikon yin hakan.

“Wannan ba zai taba samar da kasar da suke gwagwarmayar samarwa ba.

“Abin takaici ne a ce babu inda ya ke da tsaro a kasar nan, daga ayyukan ‘yan fashi, ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, ko ina ka shiga ba zaman lafiya, kuma mahukunta sun gaza daukar mataki sai aikin fitar da sanarwar Allah wadai,” inji kungiyar Kiristocin.

CAN ta kuma bukaci jiga-jigan siyasa, shugabannin addinai da sarakunan gargajiya na Ndigbo da su ta shi tsaye wajen kawo karshen ta’addanci a yankin Gabashin kasar don daina zubar da jini da tashin hankali da su ke haddasa koma baya ga tattalin arziki da walwalar yankin.