✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Jibiya: Ku dauki makami ku kare kanku —Masari

Gwamnan Katsina ya ce dole mutane su daina tsoron ’yan bindiga.

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya yi kira ga jama’ar yankin da ’yan bindiga suka addaba da su tashi tsaye tare da daukar makamai wajen kare kansu daga hare-haren bata-garin.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na Yada Labaran gwamnan, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar.

  1. Mahara sun kashe mutum 37 a Nijar
  2. Na so a ce ’yata ta kammala karatu kafin ta auri dan Buhari – Sarkin Bichi

Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a garin Jibiya a ranar Talata, a lokacin da ya je ziyarar domin jajantawa kan rasuwar mutum 10 da jami’an Hukumar Kwastam suka kashe ta hanyar tukin ganganci.

Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane sun mika wuya ga ’yan bindiga ba tare da yin wani yunkuri na kare kansu ba, inda ya ce ba komai ne jami’an tsaro za su iya yi ba.

“Kuskure ne a ce mutane sun buda kofa ga ’yan bindiga ta yadda har za su ci galaba a kansu.

“Ya kamata mutane su yaki zuciyarsu su daina tunanin cewa duk wani sha’anin tsaro hurumin gwamnati ne kadai,” a cewar sanarwar.

Sannan ya tabbatar wa da jama’a cewar gwamnatin jihar na daukar dukkan matakan shari’a wajen kwatowa iyalan wanda suka mutu a sanadin hatsarin na Kwastam hakkokinsu tare da neman diyya ga wanda suka mutu da wanda suka jikkata.

Kazalika, ya kara da cewa tuni masana suka shigar da kara kan lamarin don nema wa wadanda aka zalunta hakkinsu.

Gwamna Masari ya gargadi iyalan wanda abun ya shafa da su guji daukar doka a hannunsu, domin hakan na iya kawo koma baya ga kokarin gwamnatin jihar kan kwato musu hakkinsu.

“Abin da jami’an Kwastam ke yi ba daidai ba ne, kuma ba za mu lamunta ba.

“Kada su sake ku dauki doka a hannunku a kan Hukumar Kwastam, duk abin da suka ba ku ko suka ce muku kada ku yarda.

“Duk abin da suke son yi muku su yi muku shi a fili, ba a boye ba.

“Idan har kuka amince da wani abu a boye, to za ku kawo koma baya ga kokarin da gwamnati ke yi na ganin an kwato muku hakkinku.

“Amma idan kuka tsaya a kan bakarku, dole hukumar ta sake tunani kan yadda ta ke al’amuranta,” inji shi.