✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Sakkwato: Masarautar Bichi ta shirya addu’o’i na musamman ranar Juma’a

An ware safiyar Juma'a domin gudanar da sallah da addu'o'in samun zaman lafiya a Najeriya

Masauratar Bichi ta ware ranar Juma’a domin gudanar da sallah da addu’o’i na musamman domin neman samuwar zaman lafiya a fadin Najeriya.

Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, ne ya ayyana ranar a sakon ta’aziyyarsa gami da bayyana takaicinsa kan kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa matafiya a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato a makon jiya.

Sanarwar da Masarautar Bichi ta fitar ta hannun Sakatarenta, Alhaji Abubakar Ibrahim Yakasai, ta ce, “Mai Martaba Sarki na umartar daukacin al’ummar Bichi da su fito domin halartar addu’o’i na musamman a safiyar ranar Juma’a, 17/12/2021 a Babban Masallacin Bichi domin yin salloli tare da mika wa Allah bukatunmu;

“Za mu gudanar da addu’o’i na musamman, mu roki Allah Ya kawo mana dauki a wannan yanayi da muka tsinci kanmu a ciki, Ya kawo wa al’ummarmu zaman lafiya da za su samu damar ci gaba da gudanar da harkokinsu ne neman halaliya.”

Sanarwar ta kuma mika gaisuwar ta’aziyyar masarautar da daukacin al’ummar Bichi ga Gwamnatin Jihar Sakkwato da Fadar Sarkin Musulmi da al’ummar Jihar Sakkwato da ta Musulmi kan kisan gillar da aka yi wa matafiyan.