Kisan Zabarmari: Tambuwal da Zulum za su yi aiki don gano mamata | Aminiya

Kisan Zabarmari: Tambuwal da Zulum za su yi aiki don gano mamata

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya nuna damuwarsa tare da yin jaje a kan kisan gillar da maharan Boko Haram suka yi wa wasu ’yan Jihar Sakkwato a Jihar Borno.

Gwamnan wanda a cikin wani yanayi na tausayi ya bayyana harin a matsayin ta’asa mafi muni da cin amana ga ’yan jihar da suka fita neman halaliyarsu.

Ya kuma yi alkawalin hada karfi da Gwamnatin Jihar Borno don ganin an gano yawan ’yan asalin jihar da suke cikin wadanda aka yi wa kisan gillar da kuma bayar da tallafin gaggawa ga wadanda suka jikkata tare da taimaka wa iyalan marigayan.

Tambuwal ya nemi a kara tsaurara matakai da bin hanyoyin da suka dace wajen kawo karshen wannan matsalar don ceto rayuka da dukiyoyin al’umma.

A wata takarda da ya fitar wadda ya sanyawa hannu da kansa aka raba wa manema labarai, Tabuwal ya yi addu’ar samun rahama ga mamatan.