Kisan Zamfara: An binne mutum 143, ana ci gaba da neman gawarwaki | Aminiya

Kisan Zamfara: An binne mutum 143, ana ci gaba da neman gawarwaki

Kisan Zamfara
Kisan Zamfara
    Sani Ibrahim Paki

Akalla gawarwaki 143 ne aka binne yayin da ake ci gaba da neman wasu bayan munanan hare-haren da ’yan bindiga suka kai wasu kauyuka da ke Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara ranar Laraba.

Idan za a iya tunawa, ’yan bindigar da ke biyayya ga Bello Turji ne suka yi wa mazauna kauyukan dirar mikiya a ranar ta Laraba.

Sun kai harin ne lokacin da suke kokarin tserewa bayan jiragen yakin sojojin sama sun tarwatsasu daga dajin Fakai da ke Karamar Hukumar Shinkafi, inda suka ya da zango suka karkashe mutanen.

Mazauna yankin dai sun shaida wa wakilinmu cewa ana kwaso wasu gawarwakin ne daga cikin dazuka saboda an shammaci wasu daga cikinsu ne a gonakinsu.

Wakilin namu ya kuma gano cewa an daddatsa wasu daga cikin gawarwakin, wasu kuma an kone su, har ba a iya gane su.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Babangida, ya ce, “Wani abin takaicin shi ne hatta mata da kananan yara ba su bari ba. Sun rika tsayawa a kwararo-kwararo suna karkashe duk wanda ya fito yana kokarin guduwa.

“Daga bisani an rika zuwa ana kwaso gawarwakin mutanen. Wadanda kuma suka sha da kyar yanzu haka sun yi gudun hijira zuwa wasu yankunan, muna cikin tashin hankali matuka.

“Kauyukan da aka kai wa harin sun fi 10 saboda ’yan bindigar sun rika yawo daga kauye zuwa kauye a suna ta’asar a kan babura,” inji Babangida.

Shi ma wani tsohon soja da ya yi ritaya ya shaida wa Aminiya cewa sama da mutum 250 ne ’yan bindigar suka kashe.

“An sace shanu da sauran dabbobi kusan 2,000, sannan an kone gwamman gidaje da rumbuna. Ko da an samu zaman lafiya, to fa an tagayyara mutanen, saboda ba su da abincin da za su ci,” inji wata majiyar.

Aminiya ta rawaito cewa a ranar dai an kai wa kauyukan Kurfa Danya da Kurfa Magaji Rafin Gero da Tungar Isa da Barayar Zaki a Kananan Hukumomin Bukkuyum da Anka hari.

’Yan ta’addan sun shafe kusan sa’a 48 suna karkashe mutane suna kone gidaje da gonakinsu.