Ko daure tsofaffin gwamnoni na nuna ana samun nasara a yaki da cin hanci da rashawa? | Aminiya

Ko daure tsofaffin gwamnoni na nuna ana samun nasara a yaki da cin hanci da rashawa?

Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da yadda a yanzu kotuna ke daure tsofaffin gwamnoni, inda suka bayyana ra’ayoyinsu kan ko hakan nasara ce ga shirin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin ke yi?

 

Babu wata nasara da aka samu kan yaki da cin hanci– Auwalu Mai Siminti

Daga Hussaini Isah, Jos

Babu  shakka wannan gwamnati tana yaki da cin hanci da rashawa, amma akwai manyan mutane da suke cikin gwamnatin da ake zargin sun saci kudi, amma an kasa bincikensu a hukunta su. Ana kallonsu suna cin karensu babu babbaka. Don haka a ganina, daure tsofaffin gwamnonin da ake yi, bai nuna cewa wannan gwamnati ta samu nasara, a yaki da cin hanci da rashawa da take yi ba. Har yanzu ana cin hanci da rashawa ta ko’ina a Najeriya, ma’aikatan gwamnati ne, jami’an tsaro ne, sashin shari’a ne, duk ana nan ana cin hanci da rashawa. Don haka babu wata nasara da gwamnatin nan ta samu, kan yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

 

 

An samu gagarumar nasara – Muhammad Sahabi Mai Leda

Daga Hussaini Isah, Jos

Daure tsofaffin gwamnonin nan da aka yi, ya nuna cewa gwamnatin nan ta samu gagarumar nasara kan yaki da cin hanci da rashawa da take yi. Wannan mataki da aka dauka na daure tsofaffin gwamnonin, zai zama darasi ga gwamnonin da suke kan mulki, da masu rike da mukaman gwamnati da sauran ma’aikatan kasar nan. Sakamakon daukar wannan mataki, zai sanya kowa ya shiga taitayinsa, kan amanar al’umma da aka damka masa. Don haka a ganina an samu gagarumar nasara.

 

 

Hakan yana da kyau matuka – Buhari Lawal Baban Maheer

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Daure tsofaffin gwamnonin yana da kyau domin masu ganin ana iya cin dukiyar talakawa kuma in an ci ma din an ci bilis, tunaninsu ya sauya su gane rub-da-ciki da dukiyar talakawa matsala ce. Kasar China ba su saurara wa masu cin hanci da rashawa, abin da ke sanya doka ta yi aiki in ana hukunta shafaffu da mai, doka na hawa kan kowa yawaitar aikata laifi na raguwa.Daure su zai zama misali ga sauran jama’a a tabbata da gaske ake yi wajen yaki da cin hanci.

 

 

Tabbas an samu nasara kwarai – Alhaji Bello Garba

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Tabbas an samu nasara kwarai a kan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya domin alamomin nasarar sun bayyana a fili a fadar Shugaban Kasa da ofisoshin wasu gwamnoni da ministoci da kotu ta daure su a jarun bayan kwato dimbin kudade da kadarori da suka handama. Wannan zai yi maganin masu sha’awar aikata irin haka a nan gaba domin muna so a gyara Najeriya ce.

 

 

An samu babbar nasarar fiye da gwamnatocin baya– Ustaz Anas Yahaya Adam

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Ina ganin ya kamata mu jinjina wa gwamnatin da ke kan gado a kan fafutikar yaki da cin hanci da rashawa inda ta samu babbar nasarar da gwamnatocin baya suka gaza tabuka wa Najeriya. Idan aka ci gaba da yin hukuncin ba sani ba sabo ga irin wadannan manyan mutane kamar yadda aka yi wa wadansu gwamnoni, to ina ganin za a cimma nasarar wannan al’amari da ya shafi mahukunta a Najeriya.

 

 

Matakin da aka bi zai kara nuna da gaske ake yi – Umar Bandi Kofar Kware

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Wannan mataki da aka bi zai kara nuna da gaske ake yi ana bin matakin ne kafin a hukunta mai laifi. Da yawan mutane suna ganin kamar yaki da rashawa ta gwamnatin Buhari ba gaske ba ne sun manta da yadda dokar kasa take duk yadda ake son a hukunta mai laifi dole ne a bi yadda dokokin kasa suka shardanta kafin zartar da hukunci ko da na almundahana ne. Amma yanzu mutane sun fara tashi daga barcin da suke yi kan maganar cin hanci da rashawa sun ga yadda aka daure tsofaffin gwamnoni da suka fito a jam’iyya mai mulki sun san hakan yana nufin adalci.