✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko Liverpool za ta iya ba Madrid mamaki a Champions League?

A halin yanzu dai Liverpool na da kwallaye biyu yayin da Real Madrid ke da biyar.

Real Madrid za ta kara da Liverpool ranar Laraba a wasa na biyu na zagayen ’yan 16 a Gasar Zakarun Turai a Santiago Bernabeu.

Kungiyar Sifaniya da ta Ingila sun kara ranar 21 ga watan Fabrairu a Anfield a wasan farko, inda Real ta yi nasara da cin 5-2.

Liverpool ce ta fara zura kwallo biyu a raga ta hannun Darwin Nunez da Mohamed Salah.

Daga baya Real ta ci biyar ta hannun Vinicius Junior da ya zura biyu a raga da Eder Militao mai daya da kuma Karim Benzema da shi ma ya ci biyu.

Ko a bara a wasan karshe da suka buga a Faransa, Real ce ta ci Liverpool 1-0 ta dauki Champions League na 14 jimilla.

Liverpool ba ta kokari a kakar bana a wasannin da take yi, wadda aka fitar da ita a FA Cup, ba ta kai bantenta a League Cup ba, wanda Manchester United ta dauka.

United ta lashe kofin bayan cin Newcastle United 2-0 a Wembley, kofin farko da ta dauka a bana tun bayan kakar 2016/17 karkashin Jose Mourinho.

A makon da ya gabata ne Liverpool ta caskara Manchester United 7-0 a Anfield a wasan Premier League.

Hakan ya sa wasu ke hangen kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta koma kan ganiya, bayan wasan mako na 26.

Sai dai Liverpool ta ci karo da koma baya, wadda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Bournemouth ranar Asabar a fafatawar mako na 27.

Hakan yake nuna barakar Liverpool, wadda ke fatan karewa a cikin hudun farko a Firimiyar Ingila a kakar nan, domin samun shiga Champions League a badi.

Liverpool na fama da kalubale da yawa ciki har da na ’yan wasa da ke jinya, koda yake kungiyar ta sayar da wasu ’yan kwallo ta kuma dauko wasu a kakar nan.

Liverpool ta koma mataki na shida a Firimiyar Ingila, bayan wasa 26 da yin nasara 12 da canjaras shida aka doke ta fafatawa takwas kawo yanzu.

Tuni Klopp ya soma fuskantar kalubale, bayan da Champions League ne da Premier ya rage masa a gabansa – da kyar idan zai iya fitar da Real a Champions League a Sifaniya.

Ke nan watakila Premier League zai rage masa a gaba, wanda ba zai iya daukar kofin ba, illa ya nemi karewa a matakin ’yan hudu farko.