✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko sisi ba za mu biya diyya kan daliban Kagara ba —Gwamnatin Neja

“Ba ya cikin tsarinmu a gwamnatance biyan kudin fansa. Da irin wadannan kudaden suke kara sayen makamai.”

Gwamnatin Jihar Neja ta ce babu batun biyan diyya don karbo daliban Makarantar Sakandaren Kagara 42 da ’yan bindiga suka sace.

Gwamnatin ta kuma tabbatar da sahihancin wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na fasinjojin da aka yi garkuwa da su a motar safa mallakin Hukumar Sufuri ta Jihar Neja, NSTA ranar Lahadi.

A cikin bidiyon, an ga ’yan bindigar suna murna bayan harin da suka kai suka kama fasinjojin inda suke bukatar Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansarsu.

Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello ya tabbatar da cewa dalibai 27, malamai uku da kuma iyalansu 12 ne aka yi awon gaba da su bayan an kai hari makarantar da sanyin safiyar ranar Laraba.

“Ba ya cikin tsarinmu a gwamnatance biyan kudin fansa, saboda mun fahimci ’yan bindigar kan yi amfani da irin wadannan kudaden wajen kara sayen makamai,” inji Gwamnan.

An dai gano sunan daya daga cikin daliban da aka harbe yayin harin mai suna Benjamin Doma, wanda aka kashe yayin da yake kokarin guduwa.

Gwamnatin jihar dai ta ce akwai dalibai kimanin 650 a makarantar.

Bayan harin dai, Gwamnatin Jihar ta bayar da umarnin rufe makarantu a Kananan Hukumomi guda hudu na jihar har illa masha Allahu.

Kananan Hukumomin sun hada da Rafi da Mariga da Munya da Shiroro.