✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko sisi ba zan ba daliget ba don su zabe ni — Shehu Sani

Ya ce biyan kudi don a zabe shi ya ci karo da akidun shi

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya kuma mai neman takarar Gwamnan Jihar Kaduna a jam’iyyar PDP, Shehu Sani, ya ce ko sisi ba zai ba daliget ba don su zabe shi a zaben fid da gwani.

Shehu Sani ya tabbatar da hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, ana jajiberin ranar da jam’iyyar za ta gudanar da zaben.

Ya ce kamata ya yi daliget su fi mayar da hankalinsu wajen zaben ’yan takara masu nagarta ba masu biyan kudi ba.

A cewar shi, “Matsayina shi ne, ina cikin masu neman takarar da za su fafata gobe [Laraba] don neman kuri’un daliget.

“Amma ko sisi ba zan ba kowa ba don ya zabe ni, kuma bana goyon bayan wani ya bayar da yawuna.

“Ban yarda da siyasar biyan kudi don a zabi mutum ba, hakan ya saba da akiduna da na mutanen Jihar Kaduna.

“Ba yadda za a yi mu gina kasarmu ta hanyar ceto mutane daga kangin bauta in hanyar samar da shugabanni ta zama gurbatacciya.

“Duk masu kirana ko zaman jiran tsammanin zan ba su kudi suna bata wa kansu lokaci ne kawai. Ku yi watsi da duk wani wanda zai yi muku romon kunne da sunana.

“Ni na yarda da cin zabe ko faduwa cikin daraja,” inji Shehu Sani.

Al’adar biyan daliget kudi don su zabi ’yan takara a Najeriya dai ba sabuwa ba ce, inda wasu ma ke zargin galibi wadanda suka fi biya da yawa suke yin nasara a lokuta da dama.