✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ta kare wa Ronaldo ne?

Zuwa yanzu dan wasan ya buga wasa shida a Gasar Firimiya ta Ingila, amma bai zura kwallo ko daya ba.

A Talatar nan za a ci gaba da fafata wasannin cikin rukuni na Gasar Zakarun Turai ta bana da aka soma a makon jiya.

Wasannin da za fi daukar hankali sun hada da wanda za a barje gumi tsakanin Ajax ta kasara Netherlands da Liverpool, la’akari da cewa kungiyar mai buga gasar Firimiyar Ingila ta sha kashi a wasanta na farko da ta buga da Napoli.

Haka kuma, akwai wasan da za a fafata tsakanin Barcelona da Bayern Munich, kungiyoyi biyu da a yanzu suna kan ganiya kuma sun tara hazikan ’yan wasa da duniyar tamaula ta tabbatar da bajintarsu.

Sai dai a karon farko a shekaru 20, ana fafata gasar ba tare da wanda ya fi zura kwallo a gasar ba, wato Cristiano Ronaldo.

A watanin baya ne dan wasan na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya bayyana kudirinsa na barin Kungiyar Manchester United.

Dan wasan, wanda ya lashe Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya sau biyar ya bayyana haka ne saboda rashin jin dadinsa da rashin samun damar shigar kungiyar Gasar Zakarun Turai.

Sai dai duk da dan wasan ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar da kuma kokarin da manajansa Jorge Mendes ya yi na nema masa wata kungiyar da za ta fafata a gasar, hakan bai samu ba domin ba a samu wata babbar kungiya ba da ta taya dan wasan ba.

An yi ta tirka-tirka a tsakanin dan wasan da Manchester United, wadda ta ce ba za ta bar dan wasan ya tafi ba, shi kuma ya dage sai ya tafi, wanda hakan ya sa bai samu halartar atisaye kungiyar ba kafin a fara kakar bana.

A kakar bara, dan wasan gaban ne ya fi zura kwallaye a Manchester United, inda ya ci kwallo 24 a wasa 37 da ya buga wa kungiyar.

Bai samu kungiyar da zai je ba

Daga cikin kungiyoyin da aka yi raderadin sun so daukar dan wasan akwai Manchester City da Chelsea da Bayern Munich da Dortmund da Napoli da kuma Sporting CP ta Portugal da Atletico Madrid.

Sai dai dukkansu babu wadda aka yi wata takamaimiyar magana, sai Kungiyar Atletico Madrid, wadda ita kuma magoya bayanta suka nuna ba sa son dan wasan ya zo kungiyar.

Rashin kaunarsa da magoya bayan suka nuna bai rasa nasaba da adawar da take tsakaninsu da Real Madrid, inda a can ne kuma dan wasan ya fi haskawa da kuma irin yadda ya rika zura musu kwallaye a raga a lokuta daban-daban.

Hakan ya sa ake ganin kamar dan wasan ya yi kwantai ne domin ba a yi tsammanin za a iya rasa babbar kungiyar da za ta dauki shi ba, duk da cewa har yanzu yana zura kwallaye da dama a raga.

Kungiyar da ta fi nuna sha’awa a kan dan wasan ita ce wata kungiya a Saudiyya da ta taya dan wasan a kan sama da Fam miliyan 200, wanda da ya amsa da ya fi kowane dan kwallo karbar albashi da kusan ninkin albashin Mbappe.

Kungiyar ta sa wa dan wasan Fam miliyan 2.24 a matsayin albashinsa na mako, inda ta ce za ta dauke shi ne domin ya taka leda a kungiyar na shekara biyu, sannan ita kuma Kungiyar Manchester United za ta samu Fam miliyan 25 a yarjejeniyar.

Sai dai duk da makudan kudin da kungiyar za ta biya, dan wasan ya yi watsi da tayin domin ya fi bukatar kungiyar da zai samu damar taka leda a Gasar Zakarun Turai da aka fara.

A yanzu dai an rufe hada-hadar ’yan kwallo a Turai, wanda hakan ya tilasta wa Cristiano Ronaldo ci gaba da taka leda a kungiyar ta Manchester United daga yanzu zuwa akalla watan Disamba, lokacin da za a sake bude kasuwar musayar ’yan wasa.

Cristiano Ronaldo a kakar bana

A daya bangaren kuma, zuwa yanzu dan wasan ya buga wasa shida a Gasar Firimiya ta Ingila, amma bai zura kwallo ko daya ba.

Har yanzu bai buga cikakken wasa ba sai sau daya, domin a duk wasannin da ya buga, a benci ake jiye shi, sai daga baya ake sako shi.

Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya ce, har yanzu dan wasan bai warware ba ne kasancewar bai halarci atisayen da suka yi ba kafin a fara kakar ta bana.

Wasu magoya bayan kungiyar suna nuna rashin jin dadinsu kan yadda kocin yake ci gaba da ajiye dan wasan a benci, wasu kuma suna murna domin a cewarsu, suna cin wasanninsu duk da cewa ba ya ciki.

Ko ta kare wa dan wasan ne?

Lura da yanayin tashen da dan wasan ya yi, kuma har yanzu ake yi da shi, akwai abin mamaki a fara kakar bana, har a yi wasa shida bai zura kwallo ko daya ba.

A bangaren dan wasan PSG, wato abokin hamayyarsa, Lionel Messi ya zura kwallo uku sannan ya taimaka an zura hudu a gasar ta Faransa.

Kuma ba kamar kakar bara ba, inda idan babu Ronaldo a fili, ’yan wasan Manchester United sukan rude su gaza katabus baki daya, sannan da kwallayen da ya zura kungiyar take tinkaho, wanda za a iya cewa shi ya dauki kungiyar kacokam, a kakar bana sun ci wasa uku duka kuma a benci ake ajiye shi, sai daga baya yake shigowa, kuma bai zura kwallo ba.

Idan kungiyar za ta iya ci gaba da nuna kwazo a haka, sannan ta ci gaba da zura kwallaye tana samun nasara a wasannin da take bugawa ba tare da dan wasan ba, shin kungiyar za ta tursasa kanta dole sai ta rika fara wasa da shi?

Ko kuwa kungiyar za ta daina katabus ne, sai dan wasan ya fara zura kwallaye yana taimakonta tana samun nasara?

Wannan da ma sauransu lokaci ne kawai zai nuna nan gaba lokacin da gasar ta Firimiya ta yi zafi da kuma yadda Gasar Europa da kungiyar take fafatawa za ta gudana.