✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Duniya: Shugaban NFF na fuskantar matsin lambar sauka daga mukami

Kiran ya biyo bayan gazawar Najeriya na shiga Gasar Cin Kofin Duniya na 2022

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), Mista Amaju Pinnick, na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan ya gaggauta sauka daga mukaminsa.

Hakan dai ba ya rasa nasaba da gazawar da manyan ’yan wasan kwallon kafar Najeriya na Super Eagles suka yi na sanar wa kasar tikitin shiga gasar cin Kofin Duniya na 2022 da za a yi a kasar Qatar.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talata, 29 ga watan Maris din 2022 ne zakarun na nahiyar Afrika har sau uku suka tashi kunnen doki 1-1 da Black Stars na Ghana a wasan neman cancanta shiga gasar.

Rashin samun nasarar kungiyar Super Eagles dai bai yi wa miliyoyin ’yan Najeriya dadi ba, ciki har da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.

A lokacin dai, dubban ’yan kallon wasan ne dai suka mamaye filin wasa na Kasa na Moshood Abiola da ke Abuja domin bai wa ’yan wasan kwarin gwiwa da goyon baya ga Kungiyar.

Sakamakon haka, bayan wasan ya kare sai wasu daga cikin magoya bayan da suka kasa jurewa radadin rashin samun nasarar da suka yi, suka shiga cikin filin wasa tare da lalata kayayyakin da ke filin wasan.

Haka kuma ’yan wasan ba su tsira ba, saboda wasu fusatattun magoya bayan sun yi yunkurin kai musu hari, amma an hana su sakamakon shiga tsakani da jami’an tsaro da ke bakin aiki suka yi a kan lokaci.

A ci gaba da bin diddigin, nan take akasarin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa suka yi kira ga Shugaban NFF, Pinnick da shugabannin hukumarsa da su yi murabus ba tare da bata lokaci ba, saboda sun dora laifin gazawar Super Eagles a kan rashin ingantaccen shugabanci na hukumar.

Duk da haka, maimakon shugabannin hukumar su yi murabus, sai suka yanke shawarar ajiye Kocin kungiyar, Austin Eguavoen, da ma’aikatansa.

Hukumar NFF ta dakatar da nadin ma’aikatan hukumar tare da bayyana cewa, nan da wani dan lokaci kadan za a nada sabbin kociyoyin da za su jagoranci manyan ’yan wasan kasar.

Matakan gazawar Super Eagles

Ga wadanda suka yi imanin cewa Pinnick da takwarorinsa ne ke da alhakin gazawar Super Eagles, korar Eguavoen da mataimakansa ba wani abu ba ne illa dabarar karkatar da su.

Don haka ake ci gaba da kiraye-kirayen ya yi murabus daga mukaminsa.

Irin wadannan ’yan Najeriya sun ji takaicin yadda baya ga rasa tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2022 da zai zama abin alfahari ga kasa, rashin da’a na NFF ya jawo wa kasar asarar sama da Yuro miliyan 12.2, kwatankwacin Naira biliyan 5.6, wanda Hukumar Kwallon Kafa za ta samu idan da Super Eagles ta samu gurbin shiga gasar 2022 na cin kofin duniya.

Duk da matakan tsuke bakin aljihu da Shugaban NFF ya dauka na kwantar da hankulan masu ruwa da tsaki a fusace, matsin lambar da ake yi masa na barin ofishin na ci gaba da kara jefa shi cikin wani hali.

Daga cikin wadanda suka fara kiran yin murabus din Pinnick, har da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFA) a lokacin, Dokta Tijjani Yusuf, wanda ya ce da a wasu kasashen ne, da tuni Shugaban na NFF ya yi murabus.

A wata tattaunawa ta musamman da Aminiya ta yi da masu matsa lambar sun ce, “Wannan ne lokacin da gwamnati za ta shigo cikin lamarin, a halin da ake ciki, wanda ya kamata ya fara mika takardar murabus dinsa cikin girmamawa shi ne Shugaban NFF.

Rashin gazawar da ta gabata da yin kira ga Pinnick ya yi murabus

Wannan dai ba shi ne karon farko da ’yan Najeriya ke kira ga Shugaban NFF da ya yi murabus ba.

Idan ba a manta ba, an yi irin wannan kiraye-kirayen a baya lokacin da ’yan wasan Super Eagles suka gaza kai wa ga samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka na 2015 da 2017.

Kungiyoyin maza da mata na kasa suma sun kasa samun tikitin shiga Gasar Olympics ta Tokyo 2020, bayan Golden Eaglets da Flying Eagles sun gaza iya shiga gasar cin kofin duniya daban-daban.

A kowane hali, ’yan Najeriya da suka fusata sun yi kira ga Shugaban NFF ya yi murabus.

Sai dai duk da haka, ya ki daukar hanyar yin hakan cikin girmamawa.