✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Zakarun Turai: Za a kece raini tsakanin Barcelona da Lyon a wasan karshe

Sau daya kacal aka ci Barcelona a bana.

Kungiyoyi 72 ne suka samu halarta tare da buga wasannin Kofin Zakarun Turai na mata a bana.

Sai dai biyu ne kadai daga cikinsu suka samu kaiwa zagaye na karshe na cin kofin, wanda za a buga a ranar Asabar a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Barcelona da ke kasar Andalus da kuma da Lyon da ke kasar Faransa.

Kungiyar Barcelona ce ta lashe kofin a shekarar da ta gabata bayan ta yi nasara akan kungiyar Chelsea da ci 4-0 wanda shi ne karo na farko da kungiyar ta taba cin wannan kofin na Zakarun Turai, inda a bana za ta yi kokarin ganin ta kare kambunta.

Hakazalika ita ma kungiyar Lyon za ta yi kokarin ganin ta lashe wannan gasa, inda nasararta za ta bai wa kungiyar damar lashe gasar karo na takwas kuma mafi yawa a tarihi.

Ana tunanin dai wannan wasan karshen da za a buga a tsakanin wadannan kungiyoyin biyu zai kasance mafi zafi da aka jima ba a yi ba, duba da yadda wadannan kungiyoyin suke taka leda a kakar wasannin bana.

A kakar wasanni ta wannan shekarar, kungiyar Barcelona ta yi nasarar cin dukkan wasanninta da ta buga 30 a gasar Laliga ta mata ta kasar Andalus, inda kungiyar ta ci kwallo 159 sannan aka saka kwallo 11 kacal a ragarta.

A bangare guda kuma na tarihin wannan gasa, kungiyar Lyon ta mata ita ce kungiyar da ta fi kowacce kungiya lashe wannan kofin na Zakarun Turai domin kuwa ita kadai ta lashe har sau bakwai.

Ko a shekarar 2019 sai da wadannan kungiyoyin suka hadu a wasar karshe na Kofin Zakarun Turan, sai dai Lyon ce ta samu nasara akan Barcelona da ci 4-1 wanda ya ba ta damar lashe gasar a karo na bakwai.

Tun daga wannan lokacin Barcelona ta sauya salon taka ledarta, inda masu sharhi kan al’amuran kwallon kafa ke ganin cewa za ta iya samun nasara akan Lyon duba da sau daya ne kacal aka samu nasara a kanta a kakar wasannin bana.

Jerin sunayen ‘yan wasan da ake sa kungiyoyin biyu za su fara taka leda da su.

‘Yan wasan da ake sa ran Barcelona za ta fara da su:
Panos; Torrejon, Paredes, Leon, Rolfo; Bonmati, Guijarro, Putellas; Hansen, Caldentey, Hermoso.

‘Yan wasan da ake sa ran Lyon za ta fara da su:
Endler; Carpenter, Renard, Mbock, Bacha; Henry, Egurrola, Horan; Cascarino, Macario; Hegerberg.

Za a buga wannan wasar a filin wasar kungiyar kwallon kafa ta Juventus a ranar Asabar, 21 ga watan Mayun 2022, da misalin karfe 6 na Yamma.