✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kokarin Cire Shugaban INEC: Jam’iyyu adawa sun yi zanga-zanga a Abuja

Gamayyar jam’iyyun hamayya sun yi wata zanga-zangar nuna rashin amincewarsu kan kokarin cire Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu. Gamayyar jam’iyyun sun…

Gamayyar jam’iyyun hamayya sun yi wata zanga-zangar nuna rashin amincewarsu kan kokarin cire Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu.

Gamayyar jam’iyyun sun yi zanga-zangar ne a kofar Ofishin Jakandacin Amurka da Birtaniya da ke Abuja.

A hirar sa da ’yan jarida a yayin zanga-zangar, shugaban gamayyar, Ikenga Ugochinyere, ya ce laifin Shugaban INEC a wurin masu son ganin bayansa shi ne, shirin amfani da na’urar BVAS, wacce za ta hana magududin zabe a 2023.

Kakakin ya ce, wadanda suke da wannan aniyar tuni har sun yi yunkurin lalata na’urar ta BVAS, don haka suke son a cire Farfesa Mahmoud din.

Don haka, ya ce, masu zanga-zangar suka zo ofisoshin jakadojin na Amurka da Britaniya da kuma Tarayya Turai domin su taimaka su farauto wadannan masu bakar aniyar a duniya duk inda suke.

“Su da iyalansu, da wadanda su ka hada baki da su, su kuma hana musu izinin biza, sannan su kuma kwace dukiyoyin su

“Wadannan mutane suna so su ci gaba da mulki ko ta halin kaka, ta hanyar magudin zabe domin su kwashe dukiyar al’umma…

“Idan aka yi musu haka, zai koya musu hankali, ya kuma zama darasi ga sauran, hakan kuma zai sa dimokuradiyyar ta dore,” In ji shugaban gamayyar.

Kungiyar gamayyar ta kuma yi kira ga kasashen da su sa ido kan kokarin da Najeriya take yi na sauyin gwamnati ta hanyar zabe, wanda wasu ke kokarin kawo cikas.

Sun kuma zargi wani gwamna daga Kudu maso Gabashin Najeriya da zama a kan gaba a kokarin kawo matsala a zaben mai zuwa.

Wakilan Jam’iyyun PDP da LP da kuma AA da naga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zangar.