✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kona ofisoshin INEC na barazana ga zaben 2023 –Yakubu

Shugaban INEC ya koka kan yadda bata gari ke kone ofisoshin hukumar.

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Mahmoud Yakubu, ya bayyana damuwa kan yawan hare-haren bata-gari a kan ofisoshin Hukumar a shiyyar Kudu-maso- Gabashin Najeriya.

Yakubu, ya bayyana hakan ne a taron gaggawan da INEC ta shirya wa kwamishinonin zabe a Abuja.

“Tabbas wadannan hare-hare na haka kawai na iya tarnaki ga duk kokarin INEC tare da zubar da kimar tsarin zaben baki daya,” inji shi.

Ya yi bayanin ne bayan an kona wani ofishin INEC a Jihar Ebonyi a ranar Laraba, wanda shi ne irinsa na shida da aka kai wa ofisoshin Hukumar a Kudu-maso-Gabas.

Yakubu ya ce hare-haren barnata dukiya ne, musamman a halin da ake ciki na koma bayan tattalin arziki.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara himmatuwa wajen kare kadarorin gwamnati, musamman wadanda da suka shafi zabe.

Ya sake kira ga jama’ar gari su zage damtse wajen ba da kariya ga kadarorin da bata garin ke lalatawa.

Harin baya-bayan nan sun hada da wadanda aka cimma wuta a ofisoshin INEC uku wuta a jihar Ebonyi a ranar Laraba.

Ofisoshin su ne na kananan hukumomin Ezza ta Arewa da Izzi.

Kakakin INEC a jihar, Cornelius Ali, ya ce bata garin sun kone ofisoshin tare da injinan wuta da rumfunan zabe da wasu muhimman kayayyakin zabe.

Ya ce shugabannin Hukumar sun kai ziyarar gani da ido zuwa ofisoshin da gobarar ta shafa ne da nufin sanin girman barnar da aka yi.

Sai dai ya kwantar da hankali kan fargabar da ake yi kan ko hakan zai kawo barazana ga shirin da ake yi na gudanar da rajistar masu zabe wanda za a yi fara a watan Yuni.

Ali ya ce, “A safiyar yau, mun samu rahoton cewa wasu mutane sun kai hari tare da banka wa ofisoshinmu na kananan hukumomin Ezza ta Arewa da kuma Izzi wuta, suka lalalata muhimman kadarori.

“Da muka je can, mun ga an kona gine-ginen da ofisoshinmu an kuma ragargaza injinan janareto da rumfunan zabe da sauran kayan INEC da ke cikin ofisoshin baki daya.”

Ya kara da cewa bata-garin sun ja wa hukumar babbar asara, amma hakan ba zai rage mata kwarin gwiwa ba wajen sauke nauyin da aka dora mata na yi wa jama’a aiki.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Loveth Odah, ba ta dauki waya ko amsa rubutaccen sakon da aka tura mata ba kan harin.