✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Korar ma’aikata da rage albashi’ El-Rufai zai yi da sunan rage ranakun aiki —CAN

Kungiyar ta ce babu yadda ma'aikata za su samu nutsuwa tare da iyalansu har su rungumi harkar noma, alhali ’yan bindiga na farautar mutane a…

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta zargi Gwamnatin Jihar Kaduna da neman rage albashi da korar ma’aikata ta hanyar sabon tsarinta na rage yawan ranakun aiki zuwa kwana hudu a mako.

Shugaban CAN reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, ya gargadi gwamnatin jihar da ta guji rage albashi ko sallamar ma’aikata bayan ta bullo da sabon tsarin, wanda ya fara aiki ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, 2021.

Bayan gwamnatin ta sanar da fara aiki da tsarin a ranar Litinin, Rabaran Hayab ya shawarci ma’aikatan jihar da cewa kar su yi murna tukuna, “Sai sun tabbatar da cewa nan gaba ba za su wayi gari su ji cewa an rage musu albashi ba, saboda an rage yawan ranakun aiki zuwa kwana hudu daga kwana biyar.

“Su kuma dage da yin addu’o’in ganin ba a sake korar dimbin ma’aikata ba daga yanzu zuwa karshen wa’adin wannan gwamnatin da ta jefa al’umma cikin kuncin rayuwa,” inji jagoran na CAN.

A lokacin da take sanar da sabon tsarin, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta yi hakan ne domin ba wa ma’aikatanta damar samun lokaci da iyalansu da kuma shiga harkar noma.

Amma Rabaran Hayab ya kalubalanci hujjar da cewa ta yaya ma’aikata za su samu nutsuwa tare da iyalan nasu har su rungumi harkar noma, alhali ’yan bindiga na farautar mutane a gidajensu da gonaki da manyan hanyoyi a jihar.

Ya ce abin da al’ummar jihar suke bukata daga Gwamnatin El-Rufai shi ne adalci tare da daukar cikakkun matakan magance matsalar tsaro da ke addabar jihar da gaske, ta daina yi musu dadin baki.

Rabaran Hayab ya kara da cewa kungiyar CAN za ta ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya gami da mara wa kyayawan manufofin gwamnatin jihar baya, amma hakan ba zai hana ta rika tsage gaskiya ba a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A karshe, ya shawarci Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ta rika kare mutanen jihar ta hanyar kin amincewa da duk tsare-tsaren ko kudurorin gwamnati da za su cutar da jama’ar jihar.