✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami kan Japan

An bayyana matakin a matsayin babbar takala.

A karo na biyar cikin kwanaki goma, Koriya ta Arewa ta sake harba makami mai linzami amma a karon farko cikin shekara biyar kan Japan.

Lamarin dai ya tilastawa Japan dakatar da dukkan jiragen kasa a tsibirin Hokkaido da Aomori.

An gargadi miliyoyin mazauna tsibirin Hokkaido su zauna cikin gidajensu ko kuma su nemi mafaka.

Makamin mai linzamin wanda ya ci tafiya mai tazarar kilomita 4,500 zuwa 4,600 ya fada a Tekun Pacific.

Firaministan Japan Fumio Kishida ya yi tur da lamarin inda ya bayyana shi a matsayin ganganci.

Kwamitin Tsaron Kasa na Koriya ta Kudu ya bayyana matakin a matsayin babbar takala.

Harin shi ne na biyar a ’yan kwanakin baya-bayan nan da Koriya ta Arewa ta kai don nuna rashin amincewa da kudurin kwamitin sulhu na MDD na hana harba makamai masu linzami.

Ita ma dai Amurka ta yi kakkausar suka kan Koriya ta Arewa, tana mai cewa abu ne mai matukar hadari a harba makamin mai cin dogon zango kan Japan.

Koriya ta Arewa dai ta yi gwajin makami mai Linzami kimanin sau 20 a wannan shekarar yayin da shugaba Kim Jong Un ya sha alwashin fadada makaman nukiliyarsa da kuma kin komawa kan yarjejeniyar nukiliya da Amurka.